Connect with us

RAHOTANNI

Zaben 2019: Masu Zabe Su Yi Tunani Tsakanin Gaskiya Da Karya Kafin Kada Kuri’a – Hon. Nazifi

Published

on

•Muna Alfahari Da Zaman Lafiyar Jos
•Za Mu Fara Aikin Gina Manyan Tashoshin Mota Kafin Zabe

HON. MUHAMMAD NAZIFI shi ne Kwamishinan Sufuri na Jihar Filato wanda bayan ya rike mukamin kwamishinan Watsa Labarai da Sadarwa na tsawon shekaru biyu da rabi, ya taba zama dan majalisar dokoki da ke wakilatar mazabar Jos ta Arewa a Majalisar Dokoki ta Jihar Filatoa Alif 1999 zuwa 2007. Wakiliimmu da ke Jos, LAWAL UMAR TILDE ya tattauna da shi a kan al’amuran da ke gudana a tsakanin gwamnati da wadanda take mulka a jihar, wanda a ciki ya bayyana cewa kowa ya san yau ta fi jiya a batun ci gaban da gwamnatinsu ta samar a karkashin Gwamna Lalong. A karanta hirar har zuwa karshe domin jin sauran batutuwan da ya bayyana.

Hon. Masu karatu za su so da farko ka fara da gabatar musu da kanka…
Sunana, Malam Muhammad Nazifi, ni ne Kwamishinan Sufuri na Jihar Filato, wanda a baya ni ne Kwamishinan yada labarai na jihar, kafin nan kuma na yi dan Majalisar Dokoki na Jihar Filato da kuma dai sauran abubuwa wanda aka gudanar na rayuwa kuma na taba wakilci al’umma ta a karamar hukumar Jos ta Arewa amma dai nafi dadewa a aikin karantarwa domin tun daga malamin Firamare na fara zuwa Hedimasta daga malamin Sakandare zuwa Firinsifal kafin na karkata na shiga siyasa wanda a halin yanzu nake ciki.

Kana daya daga cikin kwamishinonin farko da gwamnan jihar ya nada don su taimaka masa, ko za ka gaya mana ilimin da ka samu game da hulda da jama’a?
Alhamdu Lillahi! Hulda da jama’a ciki aka ginu domin na yi aikin karantarwa wanda ya ba ni damar yin hulda da mutane tun daga kananan yara har zuwa manya na shekara 22, ina karantarwa na kuma yi siyasa tun daga matakin unguwa domin nayi kansila har so biyu a majalisar karamar hukuma ta Jos ta Arewa daga baya na zo na shiga majalisar dokoki na jihar ka ga duk wannan harka ce da takunshi hulda da jama’a, kafin daga baya na zo na zama kwamishina. Harka ce wanda ta bukaci hakuri da juriya ka ji ka yi kamar ba ka ji ba sabo da ba yadda za ka yi ka gamsar da kowa, ba yadda za a yi kowa ya yaba maka sabo da wani yana nan dakiki da wawan kiyayyya baya ganin wani alherin da ka yi kullum, inda ka yi kuskure yake kokari ya gani don ya bata ka a idanun jama’a, kuma kasancewar na riki mukamin kwamishinan yada labarai a ma’aikatar Watsa Labarai da Sadarwa ofishin komai da ruwanka domin za ka yi hulda da jama’a daban-daban, a wannan ofis, kama daga ‘yan jarida, ‘yan sanda, ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, diribobi da sauran al’umma.

Kasancewar wannan gwamnati taku na dab da cika shekaru hudu, akwai mutane da suke ta korafe-korafe na cewa wannan gwamanati ba ta yi aikin a zo a gani ba, kasancewar kana aiki tare da gwamna ko za ka iya bayyana wa mutane irin ayyukan da gwamna ya yi na ci gaban al’umma?
Wato masu iya magana sun ce ‘makiyinka ko da damisa ka kama da ranta ka ba shi zai ce don wannan me ye ka yi’, saboda haka abokan adawa ba za su ga abu guda na kirki da wannan gwamnati ta yi ba daga sama har kasa amma azahiri shi ne kowa ya sani a Jihar Filato ba ka isa ka fito daga gida zuwa wajen aikinka ba ba ka yi wa iyalanka bankwana ka ce masu im ba ka dawo ba su bika da addu’a. Akwai lokacin da aka yi kana ji kana gani ba za ka iya zuwa masallaci ba ko coci, mutane ba su yarda da juna ba im ba ka san mutumba ba za ka yarda da shi ba shi ma ba zai yarda da kai ba amma a yanzu an wayi gari ba inda ba za ka je ba a cikin jihar Filato, yaranka za su je makaranta ba tare da kana wani fargaba ba wanda a da hatta asibiti sai da aka raba kowa ya san a nan garin Jos an raba kasuwanni wanda ya san garin nan ya san an yi haka. Mu a wajemmu ko da ba mu yi wani abu ba, dawo da wannan zaman lafiya kawai ya sa mun yi nasara domin zaman lafiya ya fi zaman dan sarki, im babu zaman lafiya ba za ka je kasuwa ba, yaranka ba za su je makaranta ba, saboda haka muna alfahari da wannan ban da wannan duk wani fanni na inganta rayuwar al’umma wannan gwamnati ta tabo shi, bangaren kiwon lafiya an taba shi, ilmi antaba shi, gyra hanyoyi ciki da wajen birnin Jos fadan gwamnatin jihar, misali akwai wurare irin su zololo jakcan cikin garin Jos da aka manta da su fiye da shekaru 25 ba a yi aikin gyara su ba da unguwanni da yawa cikin gari amma yanzu mai girma gwamna ya bada kwangilar aikinsu duk yanzu ana kan gyaransu.
Amma babban alfaharimmu shi ne mun kawo zaman lafiya a jihar nan domin da muka kama aiki mun taras da ma’aikata na gwamnatin jihar na bin bashin kudaden albashi na watanni Tara, ma’aikatan da sukayi ritaya na bin kudin fansho na watanni goma sha uku, duk mun zo mun warware wadannan basussuka, yanzu ma aikatan jihar ba mai bimmu bashi koda wata daya. Mun wayi gari mun samu makarantun gwamnati duka sun lalace mun gyara irin wadannan makarantu sama da makarantu dari hudu, mun dibi malamai sama da dubu hudu mun wayi gari mun taimakawa duk wani dalibin mu da ya gama karatun digiri dinsa ya fita a ‘first class’ mun bashi aiki kai tsaye. Mun kuma baiwa yara ‘scholaship’ don su sami zuwa Jami’a, su karo ilmi. Yanzu haka ana sayar da fom na daukan ma’aikatanda za su cike gurbin wadanda suka yi ritaya ko suka rasu, akwai abubuwa da yawa da wannan gwamnati ta yi da ba za mu iya ambata su ba.

To a kwanakin baya, gwamnati ta rarraba wa guragu da nakasassau kekunan hawa wadansu na cewa duka goma ne aka raba, wadansu na cewa hammsin, nawa ne ainihin yawan wadannan kekuna da gwamnati ta raba wa guragu kuma mene ne muradin yin hakan?
Wannan yana daga cikin fannin taimakon da ake yi wa nakasassu domin nakasassu suna cikin wadanda ya kamata a tausaya masu bisa wannan tsari kekuna daribiyar ne wadanda gwamnati ta yi tunanin kawo su don rarraba wa nakasassun jihar, amma ba duka ne suka iso yanzu ba, kuma ba goma ko hamsin ba ne aka raba su ba, a ranar da aka yi bukin tunawa da ranar nakasassu ta duniya a gidan gwamnati, an ware ‘yan mutane kalilan daga cikin wadanda aka yi masu rijista aka mika masu wadannan kekuna wadanda gwamnan jihar ya mika su don tunawa da ranar nakasassu.

Idan muka koma nan ma’aikatar sufuri inda kake jagoranci, a kwanakin baya akwai ‘yan korafe-korafe daga ‘ya’yan kungiyar sufuri ta kasa ta (NURTW), cewar wannan gwamnati ta yi fatali da harkokinsu a jihar a dalilin barin haramtattun tashoshin mota a kan manyan tituna, hatta ma a kofar babbar tashar garin Jos akwai irin wadannan tashoshi, kasancewa wanna ya shafi ofishinka me za ka ce?
Duk wata tasha da aka samu a garin Jos da kewaye ba a wannan gwamnati ne aka kafata ba, wannan gwamanati gadar ta ta yi daga gwamnatin da ta gabata kuma su suka ba su iznin gudanar da harkokinsu a kan wadannan hanyoyin, amma mu abin da muka dauka yanzu shi ne duk abin da za a yi a yi shi a bisa doka, wanna shi ne za mu yi don rage cunkoson ababen hawa a cikin garin Jos da kewaye ba tashoshin mota kawai tsarin ya kunsa ba, tsarin ya kunshi masu aiki da babura na keke napef in
Allah ya kaimu ‘yan kwanakin kadan masu zuwa za mu yi zama a majalisa domin gwamnatin jihar tana da niyyar gina manyan tashoshin mota guda hudu da za a gina su a kowane kusurwa na shiga Jos babban birnin jihar. Manyan tashoshin da za a gina din kowannensu zai iya daukar motoci fiye da dari biu kuma za a kawata su da irin gine- genen da ya dace da zamani wanda zai kunshi dakunan cin abinci da dakunan hutawa da na bahaya da fitilun haskaka wuri. Guda daya za a gina ta ne a hanyar Bauchi Gombe, daya kuma a kan hanyar Kaduna Zariya da daya a kan hanyar Abuja Keffi da daya na manyan motoci wanda akalla zai dauki manyan motoci sama da 150, saboda rage cunkoso a cikin garin Jos hedkwatar jihar.
In Allah ya so kafin zabe muke so mu fara aikin gina wadannan tashoshin, sannan daga baya mu sany dokan haramta gudanar da ayyukan haramtattun tashoshi da ke a cikin gari inda za mu tabbatar manyan motoci ba kowane lokaci za mu bari su shiga cikin gari ba kuma za mu mayar da yin rijistar motoci da Babura su koma cikin komfuta, ICt, ta yadda kowane mota ko Tasi inda duk suka yi rijista daga nan ofishina zan iya gani. Haka nan masu Babura ma zan iya sanin mai shi da wanda yake tuka babur din, yin hakan zai rage yawan almundahana da ma’aikatan gwamnati suke yi wajen tara kudaden haraji wa gwamnatin jihar saboda haka nan ba da dadewa za mu yi zama da masu tuka keke napef a jihar don mu hada kansu su zama kungiya daya da za ta yi aiki a karkashin wata ma’aikata da za mu kirkiro da ita nan ba da dadewa ba. Mun taras da matuka baburan keke napef, a jihar suna da shugabanni biyar kowa yana cin gashin kansa wannan bai dace ba.
Masu aiki da baburan hawa kuma za mu zauna mu ga unguwannin da doka za ta yarje masu su gudanar da ayyukansu ba tare da jami’an tsaro sun musguna masu ba kamar yadda yake a baya kuma za mu dauki ‘yan banga da za su yi ta kula da ayyukan masu motoci da Babura wajen tabbatar da an range yawan cunkoson ababen hawa da ake samu yanzu a cikin garin Jos, ayyukan ‘yansanda da ma’aikatan kula da ababen hawa (BIO) duk na a kan manyan hanyoyi ne ba a cikin gari ba .
Dadin dadawa kuma kwanannan mai girma Gwamna Barista Simon Bako Lalong, ya bada afurubal a sayo motocin Bus-bus, masu daukan fasinja ciki da wajen jihar har guda dari (100), wa Kamfanin Sufuri na jihar da ake kira Plateau State Reders, don inganta harkar sufuri a jihar domin mutocin da take dasu yanzu duk sun sufa akwa wanda ta shekara goma tana aiki da wanda bata da deba itace wanda ta shekara bakwai ana aiki da ita.

Hon. Kasan cewar duk lokacin da shugaban kasa zai yi jawabi wa al’ummar kasar nan sai ya tabo maganar yaki da cin-hanci da gwamnatinsa ke yi wanda sau da yawa za ka ji mutane suna cewa gwamnati ta kwato kudade da yawa ta tara, amma har yanzu ta kasa yi ma mutane aiki da su, kasancewar kana daya daga ciki mutanen da ke da dokin ganain Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sake cin zabe karo na biyu, wane bayani za ka yi wa ‘Yan Nijeriya game da ayyukan da Buhari ya yi wa al’ummar kasar nan?
To na farko dai abin da yake a jihar mu ta Filato shi ne gwamnatin tarayya kafin zuwan wannan gwamnati ko sojan da ke sanye da kaki ba ya son zuwa Maiduguri saboda tsananin rashin tsaro kuma mun taras da akwai kungiyoyi tsageru ‘yan tawaye kamar masob da ire irensu da na ‘yan tada kayar baya kamar na Boko Haram sun kafa tutocinsu a garuruwa da yawa a jihohin Borno, Yobe da Adamawa, hatta ma a nan Jos sun yi kusan isowa, duk da yake ba a sami kwanciyar hankali kwata-kwata ba, kungiyar dake tinkaron dawo da biyafra an murkushe ta babu labarinta kuma kowa ya sani a kasar nan yau ya fi jiya a kan samun zaman lafiya kasar nan, gwamnatin nan karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ta toshe duk wadansu kofofin fitar da kudi ba bisa ka’ida ba, ba kamar gwamnatin da ta gabata ba ta jam’iyyar PDP inda ta ware zunzurutun kudi har Naira Miliyan Arba’in da sunan ta bayar ne a yi wa kasa addu’a. To ka ga irin wannan almundahanan hankali ba zai dauka ba, yanzu wanna gwamnati ta kwato sama da biliyan Arba’in a irin wadannnan kudade da aka yi ruf da ciki da su kuma ta fara yin aiki da su yanzu haka ana kokarin farfado da ayyukan jiragen kasa da na sama kuma aikin jawo ruwa zuwa Arewa ya yi nisa, ga aikin tonon mai a jihar Bauch shi ma ya yi nisa ga aikin kara inganta wutar lantarki shi ma an kusa a kammala kuma kowa ya sani matsalar dauke wutar lantarki a kasar nan ta yi sauki idan aka kwantanta da na lokacin gwamanatin da ta gabata ta PDP.

To, daga karshe ga zabe ya gabato, mene ne sakonka ga ‘Yan NIjeriya?
Duk wanda ya je wajen jefa kuri’a, ya natsu ya yi tunani kafin ya kada kuri’arsa, ya tuna tsakanin gaskiya da karya, tsakanin cin-hanci da fada da masu cin-hanci, tsakanin mai rikon amana da maras rikon amana ne za yi zaben.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!