Connect with us

BABBAN BANGO

Ziyarar Ministan Wajen Sin A Afirka Za Ta Karfafa Alakar Sin Da Nahiyar

Published

on

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kai wata ziyarar aiki a wasu kasashen Afirka daga ranar 2 zuwa 6 ga watan Janairun sabuwar shekarar 2019. Wannan ziyara dai wata dadaddiyar al’ada ce ta tsawon shekaru 29 da kowane ministan harkokin wajen kasar Sin ke fara ziyartar kasashen Afirka a farkon ko wace sabuwar shekara.
Wannan mataki ya kara nuna muhimmancin da kasar Sin ta dora kan alakarta da nahiyar Afirka, da ma kasashe masu tasowa. Haka kuma matakin ya kara jaddada kudurin kasar Sin na samun ci gaba tare gami da kyakkyawar makoma.

A yayin rangadin da ya kai shi kasashen nahiyar hudu da suka hada da Habasha, Burkina Faso, Gambia da Sanegal, Wang Yi, kana mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, ya tattauna da shugabannin kasashen kan yadda za a aiwatar da matakan da aka tsara a taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) da ya gudana cikin watan Satumban shekarar 2018 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.Kasar Sin ta kara tabbatar da cewa, ita sahihiyar kawa ce kuma abokiyar hadin gwiwar nahiyar Afirka, bisa ga sahihan manufofi da irin sakamako na zahiri da imanin da take nunawa.

Bugu da kari, kasar Sin tana mutunta zabin al’ummar Afirka na bin hanyar ci gaban da ta dace da yanayinsu, haka kuma ba ta taba tilasta musu yin wani abu ko gindaya musu wani sharadi ba. Kana idan suka fuskanci wani kalubale ko matsaloli, kasar Sin ta kan nemi hanyar ba su taimako ta hanyar da ta dace ta hanyar tattaunawa da abokan huldar ta Afirka.
A shirye kasar Sin take ta taimakawa Afirka, a lokacin da bukatar hakan ta taso. Cikin gomman shekaru ke nan a jere, kasar Sin tana tura tawagar ma’aikatan lafiya zuwa kasashen Afirka domin yakar cututtuka, baya ga masana aikin gona da samar da taimakon kudi da kwarewa da take bayarwa domin farfado da ababan more rayuwa da kawar da talauci.
Sanin kowa ne cewa, kasar Sin ce ta farko da ta taimaka a lokacin da aka samu barkewar annobar cutar Ebola a yammacin Afirka da lokacin da mummunan yunwa ta shafi gabashin Afirka.
Yayin taron FOCAC na shekarar 2015 da ya gudana a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu, kasar Sin ta yi alkawarin samar da rance dala biliyan 60, kana shirye-shiryen hadin gwiwa guda 10 da ta samar sun taimakawa mazauna kasashen nahiyar.
Tagwayen titunan mota da layukan dogo da tashoshin jiragen sama da na ruwa da filayen masana’antu da kasar Sin ta gina a sassa daban-daban na nahiyar, sun taimaka wajen hade nahiyar tare da kara karfinta na masana’antu.

A bangaren musayar al’ummomi, tawagar likitocin kasar Sin, da cibiyoyin al’adu da na Confucius sun kasance manyan kafofin sadarwa wajen karfafa fahimtar juna. An kuma bullo da wani shiri na nuna fina-finai da shirye-shiryen talabijin na kasar Sin a kasashen Afirka, inda ake nishadantar da mazauna yankunan.
Ziyarar da ministan harkokin wajen kasar ta Sin ya fara a jajiberin sabuwar shekara, za ta taimaka wajen ganin an aiwatar da shirye-shiryen hadin gwiwa da aka tsara yayin taron FOCAC na shekarar 2018 da ya gudana a birnin Beijing, wanda ya shafi fannonin masana’antu, ababan more rayuwa, saukaka harkokin cinikyayya, kare muhalli, horo da kiwon lafiya.

Ana fatan shiryen-shiryen za su bude wani sabon babi kan alakar dake tsakanin Sin da Afirka a cikin shekaru uku masu zuwa da ma gaba, a wani mataki na gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin bil-Adama.
Bayan ganawarsa da takwaran aikinsa na kasar Senegal Sidiki Kaba a Dakal, Wang Yi ya bayyana cewa, abu mafi jawo hankalin al’ummomin kasashen duniya shi ne sassan biyu wato Sin da Afirka sun fi mai da hankali kan saurin gudanar da aiki yayin da suke yin hadin gwiwa a fannoni daban daban, misali bayan kammalar taron FOCAC na shekarar 2018 da ya gudana a birnin Beijing, nan take hukumar kula da aiki ta kasar Sin ta fara gudanar da aikinta bisa matakai daban daban, ta hanyar yin shawarwari da kasashen Afirka, nan gaba kuma kasar Sin za ta kara karfafa cudanya tsakaninta da kasashen Afirka, musamman ma da kasar ta Senegal wadda ita ce kasar dake jagorantar taron kolin Beijing tare da kasar Sin a fannoni shida:
Na farko, ya dace a gina kyakkyawar makomar Sin da Afirka, a halin da ake ciki yanzu, kasashen duniya suna fama da yanayin rashin daidaito, lamarin da ya kawo barazana ga dokokin kasashen duniya da tsarin gudanar da harkokin cinikayya tsakanin bangarori da dama, tarin kasashe masu tasowa su ma ba su tsira ba, kamar yadda aka sani, kasar Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, haka kuma yawancin kasashen Afirka su ma kasashe ne masu tasowa, a don haka wajibi ne kasar Sin da kasashen Afirka su hada kai tare domin gina kyakkyawar makomarsu, ta yadda za su murkushe makarkashiyar hana ci gabansu, tare kuma da kiyaye ‘yanci da muradunsu.
Na biyu, ingiza hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu wajen aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya da kuma cimma burin muradun raya kasashen Afirka nan da shekarar 2063 na kungiyar tarayyar Afirka wato AU. Kawo yanzu kasashen Afirka da yawansu ya kai 37 da kungiyar AU sun riga sun shiga shawarar ziri daya da hanya daya, kasar Sin tana son hada kai tare da aminan kasashen Afirka domin samar da karin damammakin hadin gwiwa dake tsakaninsu.
Na uku, kasar Sin za ta tsara matakan da suka dace bisa hakikanin yanayin da ko wace kasar Afirka ke ciki, yayin da ake kokarin aiwatar da sakamakon taron kolin Beijing, hakika yanayin da kasashen Afirka suke ciki ya sha bamban da juna, a don haka ya dace a tsara shiri bisa bukatunsu a fannonin samar da taimako da rancen kudi da zuba jari da sauransu.
Na hudu, sa kaimi kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka ta hanyar yin kirkire-kirkire domin samun sakamako mai gansarwa. Kasar Sin tana fatan kamfanonin kasar za su kara zuba jari kai tsaye a kasashen Afirka, haka kuma tana goyon bayansu da su gudanar da harkokinsu a kasashen nahiyar, ta yadda za a cimma burin kyautata kayayyakin more rayuwar jama’ar kasashen, tare kuma da bunkasa hadin gwiwa dake tsakanin sassan biyu a fannonin kimiyya da fasaha irin na zamani, ta yadda za su gudanar da hadin gwiwa mai inganci tsakaninsu lami lafiya.
Na biyar, za a yi kokari domin al’ummomin kasar Sin da kasashen Afirka su ci gajiyar sakamakon da aka samu yayin taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka na Beijing, har kullum, ana mai da hankali matuka kan moriyar al’umma yayin da sassan biyu suke gudanar da hadin gwiwa, a don haka matakai 8 da za su dauka za su taka rawa wajen yaki da talauci da samar da karin guraben aikin yi da kyautata rayuwar al’umma a kasashen Afirka.
Na shida, za a yi kokarin ganin sauran kasashen duniya sun gudanar da hadin gwiwa da kasashen Afirka, an kammala taron kolin Beijing cikin nasara, lamarin da ya jawo hankalin kasashen duniya matuka, haka kuma za su kara mai da hankali kan ci gaban kasashen Afirka, muna fatan za su kara zuba jari a nahiyar, tare kuma da gudanar da hadin gwiwa tsakaninsu da kasashen Afirka. A ko da yaushe kasar Sin tana nacewa ga manufar gudanar da hadin gwiwa da kasashen Afirka ba tare da wata rufa rufa ba, ya kamata a girmama muradun ci gaban Afirka, kuma ya kamata a mayar da nahiyar Afirka a matsayin babban dandalin hadin gwiwar kasa da kasa, amma ba dandalin takara na manyan kasashe ba.
A ranar 6 ga wata, Mr. Wang ya kawo karshen ziyararsa a kasashe hudu na Afirka, inda ya bayyana ra’ayinsa game da ziyararsa ta wannan karo.
Wang Yi ya ce, kullum ministan harkokin wajen kasar Sin yana kai ziyararsa ta farko ne a nahiyar Afirka a kowace shekara, wannan wani muhimmin al’amari ne a harkokin diplomsiyya na kasar Sin. Dalilin da ya sa aka yi hakan har na tsawon shekaru 29 shi ne Sin ta yi alkawari ga Afirka, kana Sin da kasashen Afirka dukkansu kasashe ne masu tasowa, su abokai ne masu nuna goyon baya ga juna da warware matsaloli tare. Ana bukatar bangarorin biyu su kara yin mu’amala da hadin gwiwa mai zurfi.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!