Connect with us

SIYASA

2019: Atiku Da Lado Sai Sun Riga Rana Faduwa A Katsina – Darakta Janar Ta Masari ‘Nedt Lebel’

Published

on

Darakta Janar ta Kungiyar yakin neman zaben Gwamnan jihar Katsina Masari ‘Nedt Lebel’ Hajiya Zainab Abdu Ghana ta sanar da cewar, jamiyyun adawa a jihar Katsina, musamman PDP zasu sake kwasar kashin su a hannun, musamman a zaben kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari da kujerar Gwamna jihar Alhaji Aminu Bello Masari a zaben 2019. Zainab wadda kuma jigo ce a jamiyyar ta APC a jihar, ta sanar da hakan ne a hirar ta da wakilinmu a Kaduna. Zainab ta ce,” kuri’un da mu Katsinawa mazan mu da kuma matan muka bai wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Gwamnan jihar Aminu Bello Masarai a zaben 2015, in sha Allahu a zaben 2019 sai Katsinawa mun ninka yawan kuri’un.” Ta ci gaba da cewa,“ za mu shiga lunguna da sakuna, kauyuka da gida-gida da ke fadin jihar don yin gangamin don mutane su fito musamman mata don a sake zabar shugabannin karo na biyu. Da take yin tsokaci a kan romon dimokiradiyya da Gwamna Masari ya samar a jihar a cikin shekaru hudun sa na mulkin sa, Zainab ta ce, “ayyukan baza su musiltuwa, domin babu fannin tattalin arzikin jihar da Dallatu bai ingata ba, musamman wadanda anyi su ne kai tsaye don ciyar da rayuwar daukacin alummar jihar.
Zainab ta buga misali da ayyukan da Masari ya yi musamman a karkara da suka hada da giggina sababbin hanyoyi da gyaran su ciyar da ilimin zamani gaba musamman na yaya mata, inganta kiwon lafiya, ciyar da rayuwar mata da matasa gaba da sauran su. Acewar Zainab, “in sha Allahu ina mai tabbatar maka cewar, 2019 APC sama da kasa a 2019 zata samu kashi tsa’in da biyar bisa dari na yawan kuri’u Katsinawa fiye da PDP, domin Katsinawa mu a shekaru hudun Dallatu mun sheda kuma mun gani a kasa.” Ta kara da cewar, PDP da yayanta a Katsina hauragiya kawai suke yi kuma ina mai sheda maka cewar dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar da dan takarar gwamna na PDP a jihar Yakubu Lado Danmarke sai sun riga Rana faduwa a jihar Katsina a zaben 2019. Ta yi nuni da cewar, alummar jihar Katsina musamman masu kishin alummar jihar da kuma jihar, musamman talakawa baza su yarda a 2019 su yarda a rude su wajen yi asarar kuri’un su masu albarka wajen zabar PDP ba, domin har yanzu suna jin tsoron komawa gidan jiya na rashin iya mulkin, wakaci ka tashi, handama da babakere da kuma danniya da PDP ta yi a baya a jihar. Acewar Zainab, “ tuni mu Katsinawa kanmu ya waye domin a baya PDP tasha mu, amma a cikin shekaru dudu na Gwamna Masari, tuni muka warke kuma mun san inda yake yi mana cewo kuma Katsinawa musamman wadada suka san abinda ya dame su ba butulu bane tunda sun gani a kasa in sha Allahu Buhari da Masari zasu sake zaba a 2019, mun shirya tsafa don kara yiwa PDP kayin da baza ta sake shurawa ba har abada a 2019 a Katsina.” Darakta Janar ta bayyana cewar, “ zamu fito kamar Farara dango mazan mu da matan mu, kwanmu da kwarkwatar mu a 2019 don kara kunya ta PDP a Katsina, kuri’un mu suna nan a adane, ranar zaben kawai muke fatan Allah ya nuna mana.” Zainab a karshe ta yi kira ga alummar jihar, musamman matasa kada su bari gurbatattun yan siyasa a jihar suyi amfani dasu don cimma wasu burukan kashin kansu wajen tayar da tarzoma a lokacin zabubukan na 2019 da kuma bayan zaben.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!