Connect with us

NAZARI

2019: Mun Amfana Da Shirin Bai Wa Mata Bashi Na BOI —Shugaban Gidauniyar GH

Published

on

Kwamared Abdullahi Gambo shi ne Shugaban sananniyar Gidauniyar (GH) da ke koyar da mata da matasa sana’oin hannu da ke a Kaduna. A tattaunawarsa da ABUBAKAR ABBA, ya yi bayani kan hadin gwiwar da Gidauniyar ta yi da Bankin kula da Masna’antu BOI don tallafawa ‘ya’yan Gudauniyar mata da matasa, na karbar bashin sana’oi daga Bankin maras ruwa na Naira 50,000 da manufar Gidauniyar da sauransu. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance:

Mene ne manufar Gidauniyar ka?

Mun kafata ne don tallafa wa matsa da mata, musamman marasa galihu da kuma matan da mazajensu suka mutu suka bar su da ‘ya’ya marayu yadda ba sai sun dinga yin watangaririya a cikin birane don yin barace-barace ba. Kuma wadanda ba su iya yin sana’o’i Gidauniyar, za ta horas da su ‘yin sana’oi. Kuma mun lura cewar ma fi yawanci idan aka yi rikice-rikice, mata musamman su ne suka fi tsintar kawaunansu a cikin halin ni ‘yasu, su ma Gidauniyar za ta ba su horon koyon sana’o’i don su zamo masu dogaro da kansu.
Har ma matan aure ba a bar su a baya domin in an koya masu sana’oin za su dinga tallafa wa musanmman mazajensu wajen tafiyar da harkokin cikin gidajensu. Duk muna yin hakan ne ta hanyar bashin da Bankin Masana’antu yake bayarwa na matsakaitan sana’oi wanda bai da wani ruwa domin a karkashin shugabancin Shugaban kasa Muhamdu Buhari, ta ware kudin bayar da tallafin sana’oi matsakaita, musaman ga mata ‘yan kasuwa da matasa da ke kasar nan.
An ce yabon gwani ya zama dole, a iya tsawon shekaru na, ban taba ganin gwamnatin da ta ke son tallafa wa talakawa sai gwamnatin Buhari.
Ni ba dan siyasa ba ne, amma mun bincika tun lokacin da aka kafa bankunan gwamnati a kasar nan ba a taba samun bankunan da ke bayar da bashin ba ruwa musaman Bankin Masana’antu sai a lokacin gwamnatin Buhari.
Hakan ne ya sanya musamman mata suka karbi tallafin bashin marasa ruwa na Bankin na masana’antu, musamman wanda yake a jihar Kaduna, gwamnatin shugaba Buhari ta ware kudin ba kadan ba da ake kira ‘ Pity Money Traders’ da ake baiwa matasa Naira 10,000 a fadin Nijeriya.

Ba ka ganin an bar al’ummar Arewacin kasar nan a baya, wajen rungumar shirin bayar da bashin na sana’oi?
Haka ne, domin a Kudancin Nijeriya, za ka ga matan su tuni sun wuce wannan tsarin na tallafin Naira 10,000, amma mu a Arewacin Nijeriya, an bar mu a baya wasu ma gani suke yi kamar yaudara ne tallafin , amma a gaskiyar Magana, an raba Naira 10,000. Su a yankin Kudancin kasar nan, har sun kai wani mataki da ya wuce na tallafin Naira 10,000 har sun kai tsarin da za a bai wa matan tallafin Naira 50,000 kowannensu. kusan Naira miliyan 175 suna kwance suna yin lumfashi a Bankin na Masana’antu da za a rabarwa da mata da kuma matasa don yin sana’o’i. Kuma a tsarin mu, akwai Amajiran makarantar Allo da zau tattauna da malaman su yadda matan da za su amfana da bashin na Bankin Masana’antu har su 5,000 za su dauki Almajiran aiki don su dinga taya su aiki su kuma matan za su dinga biyansu. Mun yi hakan ne yadda suma Almajiran zasu zamo masu dogaro da kawanan sub a sai lallai sun dogara da yin barace-baracen deman abin da za su ciyar da kawunan su ba. Akwai kuma bashin kiwaon Akuyoyi da za a bai wa matan don yin sana’ar kiwo shi ma za mu tabbatar da shirin a nan jihar Kaduna, tsari ne na shugaban kasa Buhari don horas da matan yin kiwon Akuyoyi. Akwai kuma tsarin da shugaban kasa Buhari ya fito dashi na mallakar gidaje ga alummar kasar nan, wannan Gidauniyar ta shiga tsarin kuma za mu tabbatar da shi a nan Kaduna. Bashin mallakar gidaje ne da mutane za su dinga biya kadan-kadan har su kai ga sun mallaki gidajen.

Amma naga kamar Giduniyar ku tafi mayar da hanakali ne a cikin gari, kuna tunanin fadada ayyukan ku har zuwa karkar?
Kwarai kuwa kamar yadda na gaya maka muna da rassa a daukacin jihohin kasar nan, misali a akwai a Zariya da Kafanchan da Kudancin Kaduna da Chikun a yanzu akwai mutum 5,000 da suka shiga cikin shirin Gidauniyar na sana’o’in. Muna kuma sa ran kafin karshen wannan watan na Janairu, za a rabar da bashin da bai da ruwa, wato a ranar 16 ga watan na janairu. Kuma mu da muka amfana da shirin, za mu yi gangami mu kuma daga kur’un mu sma don nunawa duniya cewar, mun samu wannan tallafinda kuma nuna goyon bayan takarar shugaban kasa Buhari karo na biyu a shekarar ta 2019. Wannan shi ne zai zam zakaran gwajin dafi da kuma nunawa cewar tabbas gwamnatin shuba Buhari ta rabar da bashin.

Wanne kira za ka yi ga wadanda suke shirin amfana da bashin maras ruwa na Bankin Masana’antu?
Ina kira a gare su su sani wannna somin tabi ne in sun karbi bashin su yi kokarin biya don amfanin yan baya kuma ya kamata su sani in har sun maido za a rubanya masu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!