Connect with us

WASANNI

A Gobe Za A Fara Gasar Firimiyar Nijeriya

Published

on

Akwai yiwuwar za a fara gasar ajin firimiya ta kasarnan a ranar 13 ga watannan na Janairu, sai dai koda anbuga wadannan wasanni ba ranar farko akwai wasannin da baza a buga suba saboda wasu dalilai.
Wasannin da baza a buga ba sune wasannin da kungiyoyin da suka hauro gasar ajin firimiya a wannan satin za su buga, sakamakon basu dade da buga gasar Super 8 da kamfanin Bet9ja ya dauki nauyi ba wadda aka kammala kwanaki kadan da suka gabata.
Ganin akwai gajiya a tattare da kungiyoyin shine hukumar dake shirya gasar ta firimiyar tace wadancan sababbin kungiyoyin kwallon kafan da suka hauro baza a fara da suba sakamakon akwai gajiya sosai a jikinsu.
Ga jerin wasannin da baza a sami damar bugasu ba a makon farko na gasar ta firimiya :

Wikki Tourists da Bendal Insurance.
Ribers United da Remo Stars.
Rangers da Niger Tornadoes.
Lobi Stars da Katsina United.
Yobe Stars da Gombe United.
Go Round da Kada Stars.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!