Connect with us

LABARAI

Aminta Da Shugabannin Kananan Hukumomi Ya Sa Gwamna Karama Mana lokaci – Shugaban ALGON

Published

on

Shugaban kungiyar shugabanin kananan hukumomin jihar Zamfara, watau AlGON Shugaban karamar Hukumar Birnin Magaji, Honarabul Muhammad Umar, wamban Birnin Magaji, ya bayyana cewa, aminta da yadda suke tafiyar da amanar al’umma ne ya sa gwamna Abdul’aziz Yari ne ya sa aka karamana wa’adin na wata hudo.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake zanta wa da wakilinmu a Gusau baban birinin jihar Zamfara.
Shugaban ALGOL ya bayyana cewa kyakkyawar dangantaka da mu’amala da muke da ita da jama’armu kuma gwamna Yari ya ga mun kasa mun tsare wajen ganin kodirinsa ya cika na ayyukan ci gaban al’umarmu ne ya sa, ya kara wa Gwamna Abdul’aziz Yari sika a kanmu na karamana wa’adin wata hudu.
Shugaban ALGON ya kuma bayyana nasarorin da suka samu a ciki mulkinsu kamar haka na samar da hanyoyi na kwalata kowace karamar hukumar hadin gwiwa da gwamnatin jiha.
Haka kuma ya ce, sun yi hanyar kwalta sama da kilomita Ashirin hatta wasu kauyukan da ba su da furojet yanzu sun samu kwalta.
Wadannan hanyoyi sun ceto al’umma daga mawuyacin halin da suke ciki Sakamakon bunkasa hanyoyin tatalin arzikin kananan hukumomi ya karu samman a karamar hukumar Birini Magaji sakamakon kwaltar da Gwamna Yari ya yi daga Kaura zuwa Daura, ya ba ni kwarin gwiwar yin kasuwar zamani da tashar mata ta zamani, a cikin karamar hukumar Birnin Magaji wanda yanzu haka daga sasan jihar nan da mawajanta ‘yan kusuwa ne ke tashigowa cikinta.haka kuma batun Ruwan sha kowace karamar hukuma ta yi rawar gani wajen samar da ruwan sha. Bangaren lafiya ma haka, kuma duk wadanan ayyukan daga cikin kason da jiha take ba shugabanin kananan hukumomin ne muke wadannan ayyukan ci gaban al’umma.
Shugaban ya tabbatar da cewa, a duk fadin kananan hukumomin jihar Zamfara, duk inda ka shiga sai an sha mamakin ayyukan da suka yi na ci gaban al’umma da tallafi ga masu.
Da ya koma batun tsaro kuwa, Honarabul Muhammad Umar ya bayyana cewa yanzu haka kowace masarauta an dauki, matasa wadanda suke kiransu Jarimai da Gora, dari biyar kuma matasa ne don taimaka wa jami’an tsaro wajen gano duk inda mafakar ‘yan ta’adda suke, kuma duk wat ana ba su alawas na Naira dubu goma sha biyar.
Yanzu haka wata uku ke nan da fara biyan su kuma an ba su mashina da kaki na aiki da takallama da yadda duk wanda ya gansu zai tabbatar da cewa ‘ma’aikata ne.
Haka kuma ana kokarin, taron kara masu sanin makamar aiki a kowace karamar hukuma don yin aikin a ilimance. Gwamna ya yi kokarin samarwa jami’an tsaro mataimaka.
A karshe, shugaban ya yi kira ga al’ummar jihar Zamfara da su kasance, masu tsaftace kawunasu daga ayyukan assha, da kuma gyara dabi’unsu da yin addu’oi na ganin Allah ya kawo zaman lafiya da karuwar arziki a jihar da kasa baki daya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!