Connect with us

MANYAN LABARAI

An Bukaci Al’umma Da Su Kara Himmatuwa Wajen Lura Da Harkoki Lafiya

Published

on

Mai rikon mukamin shugaban Karamar Hukumar Dala Alhaji Ishak Tanko Gambaga ya bayyana bukatar da ake da ita na tabbatar da shigar da yara makaranta, shugaban na wannan bayani ne alokacin taron wuni guda da aka shirya domin wayar da kan mambobin kwamitin shigar da yara makarantu domin sanin hanyoyin dogaro da kai domin ta babbatar daaiwatar shirin sanin makamar aikin wanda karamar hukumar ta Dala ta shirya tare da hadin guiwar hukumar ilimin bai daya da kuma hukumar
UNICET da DFID.
Kansilan ilimi Abdullahi Musa Madigawa wanda shi ne ya wakilci mai rikon kwaryar shugabancin karamar Hukumar ta Dala yace wannan kira ya zama wajibi idan aka yi la’akari da cewar Gwamnati kadai ba zata iya daukar nauyin al’amuran ilimi baki daya ba.
Ishak Gambaga yace bisa la’akari da yawan al’ummar mu ga kuma kalubalen matsalar tattalin arzikin kasa da ake fuskanta, ya ce akwai bukatar gudunmawa daga daidaikun mutane domin samar da abubuwan da ake bukata na kayan harkokin koyarwa a makarantun mu. Ya ce Gwamnati na
yin bakin kokari domin inganta harkar ilimi ta hanyar bayar da horo,
daukara nagartattun malamai a makarantun mu na firamare.
Mai rikon shugabancin karamar Hukumar ta Dala ya godewa hukumar ilimi bai daya,UNICEF da DFID bisa wannan kokari na shirya wannan horaswa wanda ya ce za ta taimaka kwarai da gaske ta fuskar wayarwa da mambobin kwamitin kai ta yadda zasu aiwatar da tsarin.
Saboda haka sai ya tabbatar da aniyar Karamar Hukumar ta Dala wajen samar da dukkan
abubuwan da zasu taimaka wajen samun kyakkyawan sakamako.
Da yake gabatar makala alokacin taron mataimakin daraktan sashin ilimin manya na Hukumar ilimi bai daya na Jihar Kano Malam Musa Wada cewa ya yi an shirya wannann taro ne domin wayar da kan mambobin kwamitin na kananan hukumomi goma sha biyar na Jihar Kano.
Kamar yadda mai Magana da yawun Karamar Hukumar Dala Malam Haruna Gunduduwa
ya shaida wa Jaridar Leadership Ayau Asabar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!