Connect with us

LABARAI

An Bukaci Shugabanin Sashi-Sashi Na ATAP Su Yi Aiki Don Daukaka Darajar Kwalejin

Published

on

An bukaci dukkan ma’aikata a cikin Kwalejin kimiyya da fasaha ta gwamnatin jihar Bauchi wato ‘Abubakar Tatari Ali Polytechnic’ da su himmatu ka’in da na’in wajen gudanar da nagartattun ayyukan da suka dace da kuma yin aiki mai armashi da zai kai ga samun daukaka darajar Kwalejin fiye da inda take kai a yau.
Shugaban kwalejin, Dakta Suleman Muhammad Lame, shine ya yi wannan bukatar a lokacin bikin rantsar da sabbin shugabanin sashi-sashi (Deans) na makarantar, wanda aka gudanar a ranar Alhamsi din nan.
Dakta Suleman Lame ya shaida cewar kwalejin a halin yanzu tana gayar amfana da kuma cin moriyar goyon bayan da gwamnatin jihar mai ci a halin yanzu take basu, don haka ne ce dole ne a nasu bangaren su tabbatar da yin duk mai iyuwa domin ita ma gwamnatin ta samu nasarar cimma muradunta da manufofinta na kyautata jihar, ya jeru wasu muhimman abubuwan da gwamnatin jihar ta taka rawa wajen daukaka darajar makarantar, yana mai cewa gwamnati mai ci ta tabbatar da sahalewa da neman tantance kwasa-kwasai da dama a kwalejin, hadi da samar da gine-gine da ya kawo ci gaba gagaruma a cikin kwalejin.
Har-wa-yau, shugaban, ya kuma kirayi shugabanin sashi-sashi da su yi aiki kafada-kafada da shugabanin tsangaya-tsangaya da suke karkashinsu domin samun nasarar kyautata koyo da koyarwa a cikin kwalejin.
Lame ya kuma fadi kan cewar shi kofarsa a bude take ga dukkanin shugabanin sashi-sashi (Deans) na shawarori ko kuma wasu hanyoyin da za a inganta lamarun makarantar.
Da yake ganawa da ‘yan jarida jimkadan bayan rantsar da su, sabon shugaban sashin koyar da ilimin gudanarwa na kwalejin ta ATAP, Dakta Fafiz Baba ya gode ne wa hukumar gudanarwa na kwalejin a bisa yin adalci da kuma karramasu.
Dakta Hafiz ya sha alwashin cewar zai bayar da gagarumar gudunmawa wajen kyautata sashin koyar da ilimin gudanarwa, yana mai kara da cewa ya zo da wasu shirye-shiryen da zasu tabbatar da kai sashin mataki na gaba.
Shi ma da ke jawabi sabon shugaban sashin koyar da ilimin kimiyya, Malam Awwal Lamido wanda shine aka kara zaba a karo na biyu, ya ce zai sake dubiya ne kan irin gudunmawar da ya bayar a farko da kuma kara himma domin kwalliya to biya kudin sabulu.
Malam Lamido wanda kuma shine aka nada mataimakin shugaban kwalejin, ya yi amfani da damar nan wajen gode wa Allah a bisa basu hazikin shugaba Dakta Suleman Lame yana mai shaida cewar dukkanin nasarorin da ake samu yau a sa’ayinsa ne.
Sauran shugabanin sashin Deans da suka yi magana a wajen rantsar da sun, sun hada da na sashin koyar da sana’a da kerekere, Malam Magaji Adamu da shugaban sashin ilimin muhalli Malam Maigana Adamu dukkaninsu sun bukaci hada hanu da goyon baya ne daga ma’aikatan da suke karkashinsu domin cimma nasarorin.
Barista Mustafa A. Bila shine sabon shugaban sashin ke kula da reshen kwalejin da ke Azare, sai kuma Dakta Abdulmajid J. Abubakar ya zama shugaban sashin ilimin komai da ruwanka.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!