Connect with us

RAHOTANNI

An Ja Hankalin Matasa Su Guji Duk Wanda Zai Jefa Su Bata

Published

on

An yi kira ga matasa a jihar Kano kan kar su yarda wani dan siyasa ya yi amfani da su wajen neman biyan bukatar siyasarsa ta hanyar da ba ta dace ba, ko ya ba su kayan maye su yi abin da bai kamata ba.Mataimakiya ta musamman ga Gwamnan Kano.Dkt.Abdullahi Umar Gandu akan matasa da mata.Hajiya Surayya Aminu ta bayyana haka da take zantawa da manema labarai a wajen rantsarda sabbin Kwamishinoni da kuma kwamitin yakin neman zaben Gwamnan Kano da akayi a dakin taro na nadin sarauta dake harabar gidan Gwamnatin Kano.
Tace ba wata al’umma da zata cigaba ba tareda matasa da suka san kansu kuma suka san abinda suke ba,.Anaso matasa su zama nagartattu masu ilimi da sanin yakamata ta kaucewa duk wani abu da baia dace da mutunci da cigaban rayuwa ba.
Ta kara da cewa wannan ita tasa Gwamna Ganduje ko yaushe yake kulawa da cigaban matasa ta sama musu sana’oi na dogaro dakai ta basu horo da jari da ake mazansu da mata da kuma daukarsu aiki a cikin ma’aikatu da hukumomin Gwamnati daban-daban duk dan aga an kyautatawa rayuwarsu su zama masu amfanar kansu da al’ummar kano da kasa baki daya.
Hajiya Surayya tayi kira ga matasa da mata da cewa a zabe mai zuwa kada su yarda a yaudaresu da abinda bai kai ya kawo ba a wajen zabe,su tsaya su duba irin kauna da kishi da tallafi ga rayuwarsu da Gwamna Ganduje yake musu su sake bashi kuri’unsu,su kuma baiwa shugaba Buhari da dukkan sauran yan takara na APC dansu sami nasara a karo na biyu dan cigaba da ayyukanda suke.
Mataimakiyar ta musamman ga Gwamna Ganduje.Hajiya Surayya Aminu kan Mata da matasa taja hankalin masu rike da mukaman siyasa a Gwamnatin Kano da kuma sabbin kwamishinoni da aka rantsar kan su tallafawa kokarin Gwamna Ganduje ta taimakawa jama’a ta kowace fuska da zasu iya kasancewarsu sune wakilan Gwamna.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!