Connect with us

RAHOTANNI

An Samu Ingantuwar Tsaro A Shekarar Da Ta Wuci A Jihar Bauchi –Janar Yusuf Ladan

Published

on

Mai ba gwamnan Jihar bauchi shawara kan harkokin da suka shafi tsaro Birgediya janar Yusuf Ladan mai ritaya ya bayyana irin nasarorin da aka samu a Jihar Bauchi game da inganta tsaro a matsayin wata gagarumar nasara da aka samu tare da tallafin jama’ar Jihar Bauchi da kuma hukumomin tsaro da suke aiki domin ciyar da Jihar Bauchi gaba a fannin samar da zaman lafiya.
Ladan Yusuf ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke hira da wakilin mu a Bauchi inda ya yaba game da hadin kan da jama’a ke ba hukumomin tsaro a Jihar Bauchi, don haka ya bayyana cewa soja da ‘yan sanda da jami’antsaro na ciki da ‘yan sintiri da ‘yan kwamiti da ‘yan banga sun yi kokari wajen wanzuwar tsaro a shekarar da ta wuce ta 2019, saboda yana gida yakan samu ruhoton dukkan abubuwan da ke faruwa daga jama’a. Haka shi ma gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar akan kira shi a sanar da shi halin da ake ciki, amma da zarar sun sanar da hukumomin tsaro komai nisan wuri sukan kai dauki ba tare da bata lokaci ba kuma ana samun nasara wajen inganta lamurran tsaro.
Don haka ya yaba wa malamai game da addu’oin da suke yi da kuma sarakuna da jama’ar jihar bauchi suna bayar da hadin kai yadda ko tsakiyar dare mutane suna waya wa gwamna ko kuma zuwa gare shi ko da kuwa a lokacin suka ga abin da ya kama hukuma ta sani, idan ya kira jami’an tsaro ko ‘yan sintiri nan take za a tafi ko wane wajen a duba abin da ke faruwa na matsala idan ta taso kuma nan take za a kwantar da ita don haka aka samu nasara shekarar da ta wuce.
Janar Yusuf Ladan ya ja hankalin jama’a game da sabuwar matsalar da za a fiskanta a wannan sabuwar shekara saboda zabe, don haka ya bukaci jama’a su tashi tsaye musamman talawa su sani sai sun hada kai kafin a inganta tsaro a lokacin zabe da ake yi don jama’a kuma ana samar da mulki don jama’a da ci gaban su, saboda haka ya zamo wajibi a tabbatar da cewa ba a samu matsala an cutar da mutane ba. Saboda haka ya roki jama’a su natsu su gudanar da hidimar siyasa ta gaskiya kar su bari wani ya yi amfani da su wajen tayar da husuma wacce za ta aifar da asarar dukiya ko rayuwar mutane.
Don haka ya yi fatar yadda Allah ya sa yadda aka shiga sabuwar shekara lafiya ba tare da matsala ba a yi fatar ganin an fita cikin ta lafiya ba tare da an samu wata matsala da za ta haifar da asara ba. Musamman ‘yan siyasa ya kamata su fahimci duk wata hidima da ake yi ana yi ne don ci gaba da wanzuwar zaman lafiya, don haka ya bukaci da su yi taka tsantsan da rayuwar mutane, kowa ya fita ya bayyana ayyukan sa na alheri da mutane za su yarda da shi su gamsu su bashi guri’a. Amma a nisanci neman mulki ta kowane hali saboda a samu ingancin zaman lafiya da ci gaban kasa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: