Connect with us

WASANNI

Barcelona Ta Koma Neman Willian

Published

on

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sake komawa neman dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Willian, bayan da a kwanakin baya kungiyar ta nemi dan wasan amma bata samu ba.

A shekarar data gabata ne dai kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta taya dan wasa Willian kusan sau uku amma Chelsea tana yin fatali da tayin bayan da kociyan kungiyar, Sarri, ya bayyana cewa yanason aiki da dan wasan.

Rashin samun Willian ne yasa Barcelona taje ta siyo dan wasa Malcom, wanda shima dan kasar Brazil ne daga kungiyar kwallon kafa ta Bourdeaud, akan kudi fam miliyan 38 bayan ta doke kungiyar Roma wajen neman dan wasan.

Tun bayan komawar Malcom kungiyar kwallon kafa ta Barcelona dai baya buga abin arziki hakan yasa mai koyar da ‘yan wasan kungiyar yake ganin akwai bukatar ya sake siyan dan wasan gefe.

Jaridu daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona tayi alkawarin zata bawa Chelsea dan wasa Malcom da kudi kusan fam miliyan 20 jimilla kudin Willian din yakama kusan fam miliyan 50 kenan.

Sai dai kungiyar Chelsea tana ganin farashin dan wasan, mai shekara 30 yafi haka kuma batason rabuwa da dan wasan a irin wannan lokacin na watan Janairu saboda za’a shiga zagaye na biyu na kakar wasa.

Willian dai ya zura kwallaye biyu sannan kuma ya taimaka an zura kwallaye uku a wasanni 20 daya bugawa Chelsea sai dai Malcom kuwa bai zura kwallo ko daya ba a gasar laliga sannan bai taimaka ba a wasanni biyar daya buga.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!