Connect with us

RAHOTANNI

Boko Haram: majalisar dinkin duniya ta janye ma’aikatan ta 260

Published

on

Majalisar dinkin duniya ta sanar da janye ma’aikatan ta 260, wadanda ke gudanar da ayyukan jinkai a kananan hukumomi uku da ke jihar Borno, ta dalilin yawaitar hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram a jihar.
Majalisar dinkin duniya ta dauki wannan matakin, ta bakin jami’iar hulda da jama’a, a Nijeriya, Miss Samantha Newport, ranar Laraba, tare da tabbatar da cewa, yawaitar wadannan hare-haren a yankin sun shafi ayyukan ta.
Newport ta kara da cewar, babban ko’odinatan ayyukan jinkai a hukumar da ke Nijeriya, Edward Kallon, ya bayyana matukar damuwar su dangane da yadda abubuwa ke ci gaba da rincabewa, ta hanyar yawaitar hare-hare a arewa maso-gabas, wanda ya jawo jama’a kauracewa yankunan su. Ta ce, dagulewar lamarin ta kara tsananta zaman ni’ysu ga jama’a.
“Saboda hakan ya tilasta mana janye ma’aikatan mu na jinkai 260, daga yankunan kananan hukumomi Monguno, Kala/Balge da Kukawa, wadanda wannan rikicin baya bayan nan ya tagayyara, wanda kuma ya hana gudanar da ayyukan jinkai ga duban daruruwan jama’ar da ke zaune a wannan shiyya”.
A 2018, bangaren kungiyar Boko Haram mai suna ‘Islamic State West Africa Probince’ ko ISWAP a takaice, sun zartaswa Hauwa Leman da Saifura Ahmed, hukuncin kisa- wadanda dukan su ma’aikatan hukumar jinkan ce a shiyyar.
Bugu da kari kuma, gwamnatin tarayya ta gudanar da raba agajin kayan abinci na musamman ga yan gudun hijira sama da 30,000, wadanda rikicin Boko Haram ya tilasta musu kauracewa yknkunkn su, a yan kwanakin nan, da ke arewacin jihar Borno.
Raba wadannan kayan tallafin, an raba su ne ta hanyar hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA, da ke Maiduguri, ga jama’ar da suka fito daga garin Baga da ke karamar hukumar Kukawa, ta dalilin rikicin mayakan Boko Haram.
Kamar yadda shugaban hukumar NEMA ta kasa- Mustapha Maihaja ya bayyana wa manema labarai, “wannan tallafin jinkai ne na musamman da aka kebance shi ga wadannan sabbin yan gudun hijirar”.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!