Connect with us

MANYAN LABARAI

Buhari Ya Sha Alwashin Dakile Karbar Haraji Ba Bisa Ka’ida Ba

Published

on

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin cewa Gwamnatin Tarayya za ta duba batun harajin da ake karba ba bisa ka’ida ba domin magancewa don a karfafa kasuwancin bangarori masu zaman kansu a kasar nan.
Sanarwar da ta fito daga mai baiwa shugaban shawara a harkar yada labarai, Femi Adesina ta bayyana cewa shugaban ya tabbatar da hakan ne a lokacin da yake karbar bakuncin shugabannin Hadaddiyar Kungiyar Dillalan Hatsi da Shanu ta Kasa (AUFCDN) bisa jagorancin Alhaji Ali Tahir, a jiya Juma’a a fadarsa da ke Abuja.
Shugaba Buhari ya fada masu cewa gwamnatinsa tana da kudirin magance karbar haraji ba bisa ka’ida ba a kasar nan duk da cewa “idan wani abu ya zama jaraba yana da wuyar bari”.

Shugaban kasan yana mayar da jawabi ne game da rokon da kungiyar ta yi ma sa a kan bukatar da ake wa Gwamnatin Tarayya ta kawo dauki kan muguwar dabi’ar ta karbar haraji barkatai, yana mai cewa, “na ji mamaki sosai da na gano cewa har yanzu ana karbar haraji ba bisa ka’ida ba. Muguwar dabi’a tana da wuyar bari lokaci guda. Amma ina tabbatar muku da cewa za mu zaburad da hukumomin da suka dace game da ayyukansu na magance wannan muguwar dabi’ar tare da kiyaye mutane irinku da suke gudanar da halastattun harkokin kasuwancinsu.
‘‘Zan duba duk bukatu da koken da kuka gabatar mani domin yin wani abu a kai a lokacin da ya dace kuma a tare da gwamnatocin jihohi, za mu cim ma burinku”, in ji shi.
Da yake bayyana kungiyar a matsayin mai matukar muhimmanci ga ci gaban tattalin arzikin kasa, shugaban kasan ya fada wa wakilan cewa, “kayan da kuke kasuwancinsu su ne ginshikin ko wane tattalin arziki. Babban arzikin da kasar nan take tinkaho da shi; shi ne noma da kiwo.”
Daga nan, sai ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yin bakin kokarinta wajen bunkasa sashen, tare da nunar da cewa wasu kasashen da suka samu ci gaba irin su Ajantina, Astaraliya, Newzilan
da Danmak, sun gina tattalin arzikinsu ne da kasuwancin noma da kiwo.
Dangane da zaben 2019 kuwa, Shugaba Buhari ya ce yana lale marhabin da goyon bayan da gwamnatinsa za ta samu daga gare su, yana mai bitar cewa sun ba shi goyon baya a lokacin da ya yi takara a 2015 har zuwa lokacin zabe.
A jawabinsa, babban sakataren kungiyar, Alhaji Ahmed Alaramma, ya bayyana cewa za su yi aiki tukuru wajen ganin shugaban ya ci zabensa na wa’adi na biyu saboda irin kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen dora kasar nan a kan turbar ci gaba mai dorewa.
Dangane da batun karbar haraji ba bisa ka’ida ba, Alaramma ya ce “wasu mutane da ba a san daga inda suka fito ba sun kafa shingaye a manyan tituna daban-daban musamman a jihohin Adamawa, Taraba, Benuwai, Kuros Ribas, Ebonyi, Abiya, Inugu, Imo da Bayelsa suna cin karensu babu babbaka, kuma wannan yana ci gaba da kassara mana harkokinmu na kasuwanci”.
Ya yaba wa Gwamnatin Shugaba Buhari bisa irin ci gaban da aka samu a aikin layin jirgin kasa na Ibadan zuwa Legas, kana kungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta kafa kasuwar sayar da hatsi da dabbobi zalla a wani yanki da ke kusa da titin mota da tashar jirgin kasa a keayen
babbar hanyar Legas zuwa Ogun.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!