Connect with us

WASANNI

Dalilin Daya Sa Liverpool Ba Za Ta Iya Lashe Gasar Firimiya Ba

Published

on

Wani rahoton masana wasanni na nuni da cewa tazarar da ke tsakanin Jagora a gasar Firimiya Liverpool da kuma Manchester City shi ne mafi karantar tazara da aka taba fuskanta cikin shekaru 20 tsakanin jagora da mai bi mata baya bayan doka wasanni 21.
Batun da rahoton ke cewa abu ne mai wuya kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta iya cika burinta na dage kofin wanda rabonta da shi tun a shekara ta 1990 sai dai kuma yanayin kungiyar take buga wasa akwai alamun zata iya kai bantanata.
Rahoton ya ce hazakar da kungiyoyi 4 na saman teburi ke nunawa alamu na cewa kowacce daga cikinsu za ta iya dage kofin dai dai lokacin da ya rage musu wasanni 17 su karkare gasar ta wannan shekarar.
Ilahirin kungiyoyin hudu da suka hadar da Liverpool da Manchester City da Tottenham da kuma Chelsea na da tazarar maki 10 ne kacal tsakaninsu sabanin yadda aka saba samu a baya na akalla tazarar maki 12 tsakanin jagora da mai bi mata baya musamman a irin wannan lokaci da aka kai rabin gasar.
Haka zalika rahoton ya bayyana gasar Firimiya ta bana a wadda kungiyoyi basu samu wadataccen maki ba musamman maki 10 da Huddersfield ke da shi wanda shi ne mafi kankanta da wata kungiya ta samu a kakar wasa 11 bayan doka wasa 21.
Sai dai a kwanakin baya kociyan kungiyar Liverpool ya bayyana cewa wannan shekarar ta Liverpool ce kuma zasu cigaba da dagewa wajen ganin sun kafa tarihi a wannan shekarar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!