Connect with us

LABARAI

Gwamnati Ta Kaddamar Da Bikin Sayar Da Takin Noman Rani Kan Naira 5500 A Kebbi

Published

on

Gwamnatin Kebbi a karkashin jagorancin Sanata Abubakar Atiku Bagudu ta kaddamar da bukin sayar da takin noman rani ga manoman jihar ta Kebbi Kan kudi Naira Dubu biyar da dari biyar kowace jikar buhun taki daya a Birnin-kebbi a jiya.
An gudanar da taron bukin kaddamar da sayar da takin ne a dakin ajiyar taki na gwamnatin jihar ta Kebbi da ke a cikin garin Birnin-kebbi da ake Kira a turance “ Badariya Depot” a jiya a Birnin-kebbi.
A jawabinsa Kan kaddamar da sayar da takin ga manoman Rani na jihar Kan kudi Naira Dubu biyar da dari biyar ga kowace jikar taki daya Kwamishina Ma’aikatar Gona na jihar Barrister Attahiru Maccido inda ya bayyana wa manema Labaru cewa “ gwamnatin jihar ta Sanya hannu ga Naira Miliyan 900 domin sayo taki don a sayar wa manoman jihar domin inganta noman rani da na damana inda ayau din nan akwai tirelolin Taki gudu 250 don Kai manoma a jihar su wadata da Kuma kara samun kwarin gwiwa na habaka aikin noman a jihar da Kuma kasa Baki daya”. Kwamishina ya cigaba da cewa an sayo taki iri biyar Kamar tirela dari da ashirin da biyar na NPK da Kuma UREA dari da ashirin da biyar su zasu baka tirela 250 kenan.
Haka Kuma yace” yanzu gwamnatin jihar tayi santoci da manoni zaya je domin ya saye taki batare da wata wahala ko damuwa ba. Santocin na a kananan hukumominsu na duk fadin jihar ta Kebbi dake da kananan hukumomi ashirin da daya a jihar. Har ilayau Barrister Attahiru yayi Kira ga manoman jihar da suyi amfani da wannan dama ta Samar musu da takin zamani a cikin sauki da Kuma rahusa na tabbatar da cewa su cigaba da inganta noman a jihar da Kuma kasa Baki daya.
Bugu da kari yace” gwamnatin jihar Kebbi zata kara sayo wani taki domin manoman dama suma su iya noma a cikin sauki idon Allah yakai mu lokacin damana lafiya. Ya Kuma kara Kira ga manoman dasu cigaba da baiwa gwamnatin jihar Kebbi a karkashin jagorancin Sanata Abubakar Atiku Bagudu da Kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari domin a kara cin gajiyar dimokwaradiyya . Haka Kuma yace” gwamnatin jihar tayi tsarin santocin ne domin kawo sauki ga manoma batare da manomi yaje gidan gwamnatin ko Ma’aikatar Gona da Kuma sauran wasu wurare da ake sayar da taki da zaisa manomi ya shawahali wurin sayen taki bulle ya wahala.
Taron bukin kaddamar da sayar da takin noman rani ya samu halartar manyan Ma’aikatar gwamantin da Kuma wasu kungiyoyin manoma na jihar da Kuma sauran su.
Hoton Kwamishina Ma’aikatar Gona na jihar Kebbi Barrister Attahiru Maccido yayin da yake mekawa wani manomi tikitin karbar takin da yasaye a wurin bukin kaddamar da sayar da takin a jiy a Birnin-kebbi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!