Connect with us

BIDIYO

Jarumi Ali Nuhu Ya Yi Bikin Shekara 20 A Kannywood

Published

on

Fitaccen jarumi kuma mai bada umarni a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Ali Nuhu ya yi bikin cika shekaru 20 a shahararriyar masana’antar shirya fina finan Hausa, wacce aka fi sani da Kannywood.

Ali Nuhu wanda ya fara fitowa a masana’antar a fim dinsa na farko mai suna ‘Abin Sirri Ne’ a 1999 ya bayyana a shafin sa na sada zumunta na Instagram a ranar Jumma’a domin inda ya bayyana hakan.

Ali Nuhu kuma Manajan Daraktan kamfanin FKD Productions ya ce tafiyar tana cike da kalubale daban daban amma Allah ya ba shi karfin gwiwar ci gaba da gwagwarmaya kuma a karshe an samu nasara.

Ya ce, “Wannan tafiyar bata kasance mai sauki ba a cikin shekaru 20, amma ina godiya ga Allah da yasa hakan ya yiwu”.

Ali Nuhu ya nuna godiyar sa ga dukan ‘yan uwa da abokansa, abokan aikin sa a masana’antar da wadanda suka kasance a dashi a kodayaushe, yaa kara da cewa, “Ga duk wanda suka taya ni murna ina so in gaya muku cewa kuna da matukar mahimmanci a gare kuma ina rokon Allah ya bani hanyar da zan iya saka mu ku.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!