Connect with us

RAHOTANNI

Karamar Hukumar Kudan Za Ta Gina Babbar Kasuwar Amfanin Gona

Published

on

Domin bunkasa harkokin noma da kasuwanci karamar hukumara Kudan da ke jihar Kaduna, karamar hukumar ta sha alwashin gina babbar kasuwar amfanin gona, domin ba wa ‘yan kasuwa da ke ciki da wajen kasar nan damar zuwa su sayi kayan amfanin gonar.
Tunanin hakan ya biyo baya ne ganin yadda karamar hukumar ke sahun gaba wajen noma kayan lambu, irin su, kwakwamba da karas da dankalin Turawa da dankalin Hausa da kuma kankana wanda al’umma ke zuwa daga ciki da wajen kasar nan su saya.
Da yake amsa tambayoyin maneman labarai kan wannan aniya ta su shugaban karamar hukumar ta Kudan din, Alhaji Shua’ibu Bawa Jaja ya ce, gina kasuwar zai sa baki daga kasashen waje su shigo karamar hukumar domin sayen kayan amfanin gona, wanda hakan zai taimaka wajen kara bunkasa harkokin kasuwanci a yankin karamar hukumar.
Haka kuma ya ce, kasancewar karamar hukumar na daga cikin sahun gaba wajen samar da kayan lambu, wanda hakan ya sa mu tunanin yadda za mu samarwa manomanmu kasuwa daga kasashen waje.
Shugaban karamar hukumar ya ce za su fara wannan shiri da gina madatsar ruwa guda a karamar hukumar domin kara bunkasa noman kayan lambun.
Ya ce, duk da yawan kayan lambun da manoman wannan yankin ke samarwa, akwai bukatar a kara karfafa musu yadda za su kara samar da amfani mai yawa.
“Muna da tabbacin cewa, manomanmu za su kara himma matukar an samar musu da kyakkywan yanayin da za su yi noman rani, saboda haka ne ma karamar hukumar ta yi tunanin samar da madatsar ruwan ga manoman.
“Idan aka kammala haka madatsar rowan, al’ummar yankin da dama za su samu aikin yi, arziki zai yalwata harkoki su kankama.
“Wannan yunkuri namu ko shakka babu zai jawo hankalin masu zuba jari daga kasashen waje, wanda hakan zai taimake mu wajen samun kai kayan amfanin gonarmu kasashen waje.”
Shua’ibu Jaja ya ce, tuni an riga an ware kudin da za a fara gudanar da wannan aiki, za kuma a fara aikin ne a cikin wannan shekarar.
“Za a yi wadannan ayyukan ne karkashin asusun kudadaen “Paris club” wanda gwamnatin tarayya ta ba karamar hukumar.
“Sabo da haka wannan aiki ba zai shafi wasu kananan ayyuka da gwamnatin tarayya za ta yi a wannan karamar hukuma ba.”
A bangaren ilima ma shugaban karamar shugaban ya tabbatar da kokarin da karamar hukumar ke yi na tallafa masa domin samar da daliban da za su samu damar karo karatu daga manyan makarantun da ke ko’ina a fadin kasar nan. Ya ce, saboda haka ne ma kwanan karamar hukumar ta samar wa dalibai ‘yan asalin yankin su 100 guraben karo karatu a manyan makarantun daban-daban kuma ta biya musu kudin makaranta tare da kudin da za su kama muhallin kwana.
Haka kuma karamar hukumar ta dauki dawainiyar daliban 100 don koya musu ilimin kwamfuta, yadda za su fuskanci jarabawar kamamla sakandire ta SSCE daNECO da ta share fagen shiga jami’a ta UTME da JAMB, wadanda su ma karamar hukumar ta dauki alkawarin cewa ida suka gama , kuma suka samu nasarar jarabawar za ta dauki dawainiyar karatunsu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!