Connect with us

MANYAN LABARAI

Matar Gwamnan Kebbi Ta Bukaci INEC Da Ci Gaba Da Wayar Da Kan Masu Zabe

Published

on

Matar gwamnan jihar Kebbi, Dakta Zainab Shinkafi Bagudu ta yi kira da a samu alaka a tsakanin hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC da wadansu masu fada a ji, domin ganin an kaddamar da shirin wayar da kan masu zabe ta hanyar nusasshe da su yadda ake zabe domin kaucewa bata kuri’a a zaben 2019.
Dk. Zainab wacce matar shugaban kasa A’isha Buhari ta zabe ta a matsayin Babbar Kodinetan mata da matasa na arewa maso yamma na Kwamitin Kamfen din shugaban kasa, ta yi wannan kiran ne a jiya a garin Birnin Kebbi a lokacin da take amsa tambayoyin manema labarai.
Ya kara da cewa; wayar da kan masu zaben wata hanya ce ta magance mutane su rika bata kuri’unsu a yayin zaben, kuma har wala yau hanya ce ta wayar da kan masu zaben akan nuna musu illar siyar da kuri’arsu, domin su samu damar zaben shuwagabanni managarta.
Ta shawarci INEC da ta hada hannu da masu fada a ji, da kuma kungiyoyin Kamfen domin ganin an fara wannan shiri na wayar da kan masu zabe.
“Amfani da Ilimi wani abu ne da INEC take aikatawa. Kuma mu ma ya kamata mu yi koyi, kungiyoyin Kamfe su ma su yi koyi da INEC.”
“INEC tuni sun saki kayayyakin neman ilimin abin, kuma tuni aka fara wayar da kai a Kebbi. Zamu tabbatar mun shirya taro ga shuwagabannin mata da na matasa, saboda su samu wadannan kayayyaki domin ganin su ilmantar da mutane yadda ake zabe.” Inji ta.
Ta roki mata da matasa da ka da su sake su siyar da ‘yancinsu, ta hanyar siyar da kuri’unsu.
“Zamu fada musu cewa da su kalli rayuwarsu ‘ya’yansu, ilimin ‘ya’yansu, da kuma walwalarsu. Nawa ne za su siyar da kuri’unsu? Naira dubu 5 ko 10? Sam kuri’arsu ta fi gaban haka.” Inji ta.
A kashe ta shawarci matasa da mata da su guji aikata dabanci tare da nisantar kansu da shaye-shaye kwayoyi, domin a cewarta matasa da mata sune abin alfaharin al’ummarnan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!