Connect with us

LABARAI

Mujami’ar EYN Ta Yi Bukin Cika Shekaru 64 Da Kafuwa A Nijeriya

Published

on

A karo na sittin da hudu, an bude babban taron kungiyar Tarayyar Ekkelesiyoyin Kristi A Nijeriya (TEKEN), ta cika shekaru 64 da kafuwa a kasar, da zai dauki tsawon kwanaki shida na gudana a jihar Adamawa.
Babban taron cocin na shekara-shekara, wanda ke gudana a hedikwatar cocin dake Kwarhi cikin karamar hukumar Hong a jihar, ya samu halartan manyan baki, wakilan cocin, rabaran-rabaran daga sassan jihohin kasar.
Da yake jawabin bude taron babban bako mai jawabi kuma shugaban cocin EYN na kasa Rabaran Joel Billi, ya ce cikin shekaru 64, cocin ya fuskanci matsaloli da dama, ya ce cocin ya’yi fama da fadi tashi, amma bai taba tunanin wata rana ba zai kaigaci ba.
Ya ci gaba da cewa “akwana a tashi yanzu wadannan matsalolin sun zama tarihi, mun cimma nasarori da dama, yanzu haka darikoki goma sha biyar ke karkashin kulawar cocin EYN” inji shi.
Da yake magana game da matsalar tsaro kuwa Billi, ya ce mambobin cocin suna fuskantar hare-haren boko haram a kullum, ya ce yara 209 cikin ‘yan makarantar Chibok da ‘yan bindigar suka sace ya’yan cocin ne, sun kuma lalata musu coci-coci da dukiyoyi.
Haka shima da yake jawabi shugaban kungiyar TEKEN ta kasa Rabaran Dakta Caleb Ahima, ya ce kungiyar ta cimma nasarori da dama, ya ce babbar nasara itace hadinkai da zaman lafiyar da take kokarin tabbatar da cewa ya wanzu a kasar.
Ya ci gaba da cewa “mun cimma nasarori a fannonin kiwon lafiya, ilimi, ruwansha, tattalin arzikin da kuma aikin abbatar da zaman lafiya a tsakanin jama’a” inji shi.
Haka kuma jama’a da dama da sukayi jawabi a taron sun bayyana kungiyar da cewa ta cimma ingantattun nasara cikin wadannan shekarun.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!