Connect with us

MANYAN LABARAI

NDLEA Ta Cafke Diloli 339 Da Ake Zargi Da Safarar Kwayoyi A Edo

Published

on

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA ta shaida cewar ta cafke mutane dari uku da talatin da tara 339 da take zargin dilolin kwayoyi ne, inda kuma ta tabbatar da cewar 38 an samu tabbacin su dilolin ne a jihar Edo cikin shekarar da ta gabata.
Rundunar ta kuma samu nasarar kama kilogiram na kwayoyi daban-daban da suka kai adadi har 45,743.19 a cikin nasarorin da suka cimma a cikin shekarar da ta gaba din.
Da yake ganawa da ‘yan jarida a garin Benin jiya, shugaban rundunar NDLEA na jihar Edo, Buba Wakawa, ya ce, matsalolin shaye-shayen miyagun kwayoyi na haifar da munanan kalubale kamar fashi da makami, garkuwa da mutane, kashe-kashe da kuma wayaitar kungiyar asiri a jihar.
Don haka ne ya ce, dole ne su ci gaba da taka wa lamarin burki domin tsaftace jihar a kowani lokaci, yana mai bayanin cewar shan miyagun kwayoyi illa ne sosai ga ci gaban kasa.
Ya ci gaba da bayanin cewar daga cikin wadanda suka samu nasarar kamewan, 271 daga cikinsu maza ne, inda kuma 68 suka kasance mata.
Wakawa ya kuma ci gaba da cewa, fili mai griman hekta 32.0975552 da ake shuga kayan maye sun tarwatsa su, inda ya ce motoci guda 12 da babura 3 da dillan ke amfani da su wajen jigilar kayen mayen sun kasance a karkame.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!