Connect with us

WASANNI

Neymar Yana Son Koma Wa Barcelona

Published

on

Rahotanni daga kasar Faransa sun bayyana cewa dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta PSG, Neymar, ya gayawa wasu daga cikin shugabannin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona cewa yanason komawa kungiyar.
Neymar dai yabar Barcelona zuwa kungiyar PSG a shekara ta 2017 inda kuma yafi kowanne dan wasa tsada bayan da kungiyar tasa ta biya fam miliyan 200 inda kawo yanzu ya zura kwallaye 46 cikin wasanni 50.
A kwanakin baya akwai rahotannin da suke yaduwa cewa dan wasan yanason komawa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona sakamakon rashin jituwa da wasu daga cikin ‘yan wasa da shugabannin kungiyar ta PSG.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa dan wasa Neymar ya tuntubi shugabannin Barcelona akan yanason komawa kungiyar kuma mahaifin dan wasan shima ya nuna cewa shi da dan wasan sunyi kuskuren barin Barcelona.
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona dai zata iya siyan dan wasan bayan da kungiyar PSG ta saba dokar yadda kungiyoyi suke kashe kudi ta nahiyar turai inda ake tuhumar PSG din da kashe kudi sama da yadda doka ta tsara.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai itace aka bayyana a kwanakin baya tanason siyan dan wasan sai dai Barcelona zatayi kokarin ganin ta mayar da dan wasan saboda kada yakoma Real Madrid.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!