Connect with us

WASANNI

Ramsey Da Juventus Sun Kulla Yarjejeniya

Published

on

Kungiyar kwallon kafar Juventus ta Italiya ta ce ta na shirye -shiryen kammala siyan zan wasan tsakiya na Arsenal, Aaron Ramsey, wanda kwantiraginsa ya kare da Arsenal din cikin wannan kaka kuma kungiyar ta gaza cimma sabuwar yarjejeniya da dan wasan a watan Satumban bara.
Matukar dai cinikin ya tabbata zai kawo karshen shekaru 10 da Ramsey ya yi a Arsenal yayinda zai zamo dan wasa na biyu mafi karbar albashi a Juventus bayan Cristiano Ronaldo da ke karbar dala dubu 179 kowanne mako.
Yanzu haka dai Juventus ta sanar da yuro miliyan 6 da rabi a matsayin farashin da za ta sayi dan wasan, yayinda kungiyoyin Turai irinsu Bayern Munich Real Madrid PSG da ma Intermilan ke zawarcinsa.
Tun a shekarar 2008 ne Ramsey ya kulla kwantiragi da Arsenal kan yuro miliyan 8 da dari 8 daga Cardiff City inda ya zura kwallaye 62 a wasanni 354 da ya bugawa Arsenal yayinda ya yi nasarar dage kofin FA a shekarun 2014 da 2015 da kuma 2017.
Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Unai Emery, ya bayyana cewa babu yadda zaiyi ya hana Ramsey tafiya sai dai yayi kokarin shawo kan dan wasab amma kuma lokaci ya kure.
Tuni shugabannin kungiyar suka fara shirye shiryen siyan dn wasan tsakiyar da zai maye musu gurbin Ramsey yayinda aka danganta kungiyar da neman dan wasan tsakiyar Sebilla, Eber Bonega.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!