Connect with us

RAHOTANNI

Rancen Da Gwamnatin Bauchi Ta Bai Wa ‘Yan Kasuwa Zai Habaka Tattalin Arziki, Inji Salisu Mai Suga

Published

on

Shahararren dan kasuwan nan da ke Bauchi kuma mai tallafawa mutane, Alhaji Salisu Garba Mai Suga ya bayyana cewar, matukar dan kasuwa yana bukatar kaiwa ga nasara a fagen kasuwancinsa to sai ya samu yarda daga abokan huldarsa.
Mai Suga ya bayyana haka ne a yayin da yake amsa tambayoyi daga wajen ‘yan jarida a game da batun lamunin naira miliyan dubu daya (N1b) da Gwamna Muhammed Abdullahi Abubakar ya amincea baiwa kungiyar gamayyar ‘yan kasuwa a jihar Bauchi domin bunkasa jarin kasuwancinsu, yana mai cewar, abin da kasuwanci yake bukata shine samun yarda a tsakanin shugabanni da ‘yan kasuwa wadanda za a basu jari domin gudanar da kasuwanci da abokan hulda, wadanda zasu sayi kaya daga hannun ‘yan kasuwar, “matukar akwai yarda a tsakani to babu ko shakka kasuwanci zai habaka kuma kowa zai ji dadi,”
Ya ce, a yanzu haka Bauchi ta zama wata cibiyar kasuwanci, duba da yadda harkokin kasuwanci suka inganta a jihar, “yau za ka ga dan kasuwa daga jihar Bajchk zai iya sayo kaya cikin tireloli fiye da guda bakwai, haka kuma ‘yan kasuwa da dama sukan tafi kasashen India, Masar, Jamus, China da kasar Amurka, dadai sauran yankuna na duniya da zummar gudanar da harkokin kasuwanci, wadannan dalilaine da suka gwada cewar, harkoiin kasuwanci a jkhar Bauchi sun inganta,” Inji shi
Alhaji Salisu ya kuma jinjinawa gwamnan jihar Bauchi bisa yadda ya baiwa ‘yan kasuwa bashin naira miliyan dubu daya (N1b) ba tare da biyan kudin ruwa ba, “Bashin zai taimaka wajen kara bunkasa harkokin kasuwanci a jihar mu”.
Ya ce ‘yan kasuwa da masu sana’o’in hannu sun bijiro da shirye-shirye daban-daban da suka dace domin rarraba naira biliyan daya da aka basu rance ta hanyar da ta dace da zumar tabbatar da cewar, dukkan ‘yan kasuwa daga kananan hukumomi ashirin na jalihar sun amfana.
Salisu Mai Sugar ya kuma ce dukkan ‘yan kasuwa da aka basu rancen zasu dawo da kudaden akan lokaci, haka kuma ya ce zasu maido da kudaden ne cikin watanni ashirin, matukar ‘yan kasuwar sun dawo da kudaden da aka basu za a yi amfani dasu wajen baiwa sauran ‘yan kasuwa da basu samu ba, kuma ya ce bisa yarda da yayi da ‘yan kasuwar, zasu maido da kudaden cikin sauki da yardar Allah.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!