Connect with us

LABARAI

Rikici Kan Tikitin Takarar Dan Majalisa: Zan Gaggauta Yanke Hukunci –Alkalin Kuto

Published

on

Lauyoyin dake tsayawa mamba mai wakiltar karamar hukumar Madagali a majalisar dokokin jihar Adamawa Emmanuel Tsamdu, da tsohon shugaban karamar hukumar Yusuf Muhammad, sun bukaci kotu da ta gaggata yanke hukunci kan tikiin tsayawa takaran kujerar dan majalisar dokoki.
Dama dai tsohon shugaban karamar hukumar ta Madagali Yusuf Muhammad, ya maka mamba mai wakiltar karamar hukumar, hukumar zabe INEC da jam’iyyar APC, gaban wata babbar kotun tarayya a jihar, biyo bayan zargin kwace mishi tikiin tsayawa takara.
Da yake yiwa kotu bayani lauyan mai shigar da kara Baresta Abayomi Akomode, ya ce zaben fid da gwanin kujerar dan majalisa da jam’iyyar APC ta gudanar ranar 7/10/2018 a jihar da jam’iyyu sukayi, wanda yake tsayawa ya lashe.
Ya kara da cewa sakamakon zaben ‘yan takaran ya nuna a fili muumin da yake karewa ya lashe, amma kuma wanda ke kan kujerar (Tsamdu), ya kawo wasu kuri’u daban yana cewa wai shine ya lashe zaben.
Lauyan mai shigar da karar ya’yi fatan kai tsaye kotu zata maido mishi da hakki ta tabbatar dashi a matsayin dan takara, ya ce aikata haka zaisa jama’a su san lallai anyi musu adalci a lokacin zaben.
Barista Akomode, ya kuma yi fatan kotun zata umurci wanda ake tuhuma na daya da biyu (APC/INEC), da su bada bayani game da tuhumar da’ake musu kowanne a lokacin da sauraren shari’ar ke gudana.
Da yake maida kalami lauyan wanda ake tuhuma Ibrahim Bawa SAN, ya ce ba zaice komai game da batun rokon da’a yiwa kotun ba.
To sai dai ya ce batun ci gaba da shari’ar cikin kwanaki biyu abin dubawa, ya ce kamata ya’yi a ci gaba da sauraro cikin sati uku, ya kuma bayyana cewa gyaran da’aka yiwa tsarin mulki bai bada daman sake zabe kafin lokacin kowani zabe ba.
Bayan da Mai shari’a Abdul’aziz Anka, ya saurari muhawar da bangarorin lauyoyin biyu sukayi, ya ajiye ranar 25/1/2019, a matsayin ranar ci gaba da sauraren shari’ar.
Haka kuma mai shari’a Anka, ya bada kwanaki goma ga duk bangarorin da gabatar bayanai karekai da kuma mai karekai na biyu ya cikakken adreshi bisa tsarin kotu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!