Connect with us

MANYAN LABARAI

Rundunar ‘Yansanda Ta Kama Mai Kera Bindigogi A Zamfara

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara karkashin jagorancin CP, Zanna Muhammad Ibrahim ta samu nasar cafke wani sharararen makerin bindiga mai suna Umar Shehu. Kwamishinan ‘yansandar jihar ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zanta wa da manaima labarai a Hedikwatarsu da ke Gusau.
Kwamishinan ya bayyna cewa ‘Umar Shehu ya shahara wajen kera bindigogi kuma yana sai da wa jama’a.
Don haka, wannna ya saba wa saboda haka zai fuskaci kuliya.
Kwamishina Zannah ya kuma bayyana nasara da suka samu na kwato wata mace daga hannu masu garkuwa da muta ne. Kuma ya tabbata da cewa rundunar sa ba za ta lamuncin yin ta’addanci ba, musamman masu garkuwa da mutane da Mahara da kuma bata-gari, zaman lafiyar su shi ne su yi saranda su kaurace wa wadannan munanan ayyuka. Idan ba haka ba lallai duk wanda ya zo hannu zai yaba wa aya zaki.
Kwamishina Zannah ya tabbatar da cewa Rundunarsa ta yi shiri na musamman a kan yadda za a gudanar da kwamfen da ‘yan jam’iyyu don ganin an yi zabe mai inganci cikin kwanciyar hankali da lumana.
Kwamishinan ya kara da cewa, ba za su lamunci bargar siyasa ba, ko yin ta’addanci da sunan siyasa.
Kuma wadanda aka kama a lokacin rikincin a karamar hukumar tsafe yanzu haka suna fuskantar shari’a.
Kwamishinan ya Kuma yi kira da babbar murya da cewa, jama’a na da gudummowar da za su ba da a harkar tsaro, inda duk su ka ga an wani abu da ha saba wa doka Ko kuma wani Abin da ba su gane ma sa ba da su gaggauta sheda wa rundunar ‘yansandan.
Da manema labarai suka tambayi Umar Shehu a kan kera bindogogi da ya ke yi ya shaida musu cewa, lallai shi ne yake kera su amma shi danbanga ne kuma mutanensu ‘yanbanga yake kera wa don su kare al’umma da su. Ya ce, bai taba sai da wa wani ba, wanda ba danbanga ba. Y ace yana sai da kowace bindiga akan Naira dubu uku.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!