Connect with us

SOYAYYA

Salon Yaudara

Published

on

Salo na yaudara kala-kala ne wani yakan iya gane wata yaudarar wani kuma ba zai iya gane wa ba, ba lallai sai namiji ko mace sun bi ta hanyar da aka saba sani ba suna iya bin hanyoyi da dama na yin yaudara koda kuwa su bada niyyar yin yaudarar sukai ba.
Wasu mazan suna iya yaudarar mata ta hanyar rashin furta musu gaskiyar al’amari duk da cewa daman ita kanta yaudara gaba daya karya ce da rashin furta gaskiya ke jawo ta, sai dai wannan hanya da zan magana akai namiji yana iya yiwa mace ita a lokacin da mahaifansa suka ki amincewa da wadda yake so ya aura ko kuma ita budurwar iyayenta suki amincewa da wanda take so ta aura rashin samun damar hakan shi yake sawa masoyin kin furta gaskiya.
Misali in namiji ne ya isar da son da yakewa yarinya wajen magabatansa suka ki amince wa suka kuma tabbatar masa da cewa wannan aure ba me yuwa ba ne don ba su amince da yarinyar ba dama auran nasu baki daya, me makon ya samu yarinyar ya sanar da ita halin da yake ciki ko da kuwa ta dabara ne dan su nisanta da juna sai ya ja baki ya tsuke ya yi shuru abinsa ba tare da ta sani ba, ya ci gaba da ba ta so da kauna har ma da tsantsar kulawa da bata mata lokaci.
Haka macen za ta ci gaba da zurfafa son da take masa ba tare da zuciyarta ta kawo komai ba face tsantsar so da kaunar da yake nuna mata, koda kuwa abin ya afku a lokacin da zuciyarta bata karasa kamuwa da shi ba ko kuma akwai so din amma beyi nisa ba, rashin sanar da ita da wuri shi zai kara sa mata sonsa a zuciya karshe kuma lamari ya canja anan ne zata gane ya yaudare ta, shi kuma lokacin zai hau kame-kame yana inda-inda don ya san bai kyauta ba.
A na sa tunanin furta mata da wuri wajen ba ta hakuri don su rabu da juna kamar cutar da ita ne ko kuma shi cutar da kansa ne tunda yana sonta wanda kuma inda zai sanar da ita da wurin da tuni ta san inda dare ya yi mata ta ruga da ta dau dangana ta kama dahir wanda ta san zai aure ta koda kuwa bata samu wani ba ta ruga da ta bar wa zuciyarta cewa ba lallai ta same shi ba tunda har ya furta mata, amma ina! Ba zai hakan ba sai ya ja zuciyarta har ta yi nisa ya kai ta inda ba za ta iya dawo wa ba.
Wannan salo ne na yaudara tunda kuwa ya riga daya san cewa ba za a yarda ya aure ta ba amma ya kasa sanar da ita da wuri ya kasa furta mata kalmar da ta fahimci cewa sui hakuri da soyayyar da suke wa junansu, ya kyale ta har sai da soyayyarsa ta gama mamaye zuciyarta baki daya sannan ya dawo ya sanar da ita wannan yaudara ce mara dadi wanda duk wanda a kai wa ba zai manta da irinta ba.
Haka ma idan macence za ta yi wa saurayin hakan tunda kuwa kowanne bangare yana taba halinsa walau mazan walau matan, kowanne yana fud da nasa salon yaudarar dan wata macen idan ta dauko nata salon sai an ruke baki duk da cewa an saba jin kalolin yaudara daga wajen matasa.
Wata macen tana iya yaudarar namiji ko nace maza da yauwa wajen amsa musu soyayyarta yayin da tasan tuni ta samu tsayayye har ma an kawo kudi duk da sanin cewa tana da kudin wani a hannu wanda magabata suka bayar ga iyayenta ko ma saka ranar aure amma hakan baya hanata ta amsawa wasu soyayyar da suka nema daga gareta.
Namiji zai ganta ya ji ta kwanta masa a rai har ya nemi yin magana da ita a lokacin ne zata kwantar da kanta har da alamar jin kunya ya isar da sakon da ke zuciyarsa ta amince ta karbi soyayyarsa suci gaba da soyayya tamkar ba tada wani tsayayye shi kuma ya saki jikinsa ya samu matar aure in ma kari yake kokarin yi da ita duk ta amince da hakan koda yaushe tana tare da shi tana sauraransa yayin da tsayayyen ya kira a gabansa in akai rashin sa’a sai ta nemi iznin daukar wayar ta dan matsa gefe guda tace masa tana zuwa tana wani aiki ne sannan ta dawo wajen wanda take yaudara taci gaba da hirarta tare da ce masa wata kawarta ce ta kira.
Haka zasu dau tsawon lokaci suna tare ba tare daya sani ba, ya kashe mata kudi taita cin kudinsa daman ita abinda take so kenan kuma in aka buncika namijin da takewa hakan ba daya bane ba kuma biyu ba suna da yawa sosai, sai lokacin da ba yadda zata yi dole ta sanar da su sannan ta fada masa cewar sai dai yayi hakuri domin kuwa an kusa aurenta saura sati kaza ayi auren, wata ma babu kunya sai tace ai be fada mata cewa sonta yake da aure ba duk a tunaninta abota kawai suke ko kuma mutunci, wannan ma wani salon yaudara ne wanda wasu suke yi, Allah dai ya kyauta.
Salon yaudara nada yawa kamar yadda na fada dan wani namijin yana da mata ba shida halin kara aure ko kuma kwata-kwata ba shida ma ra’ayin karawa matarsa aure ya fiso ya zauna da ita kwal tilo sai kuma ‘ya’yansa in ma ba shida ‘ya’ya suyi zamansu su biyu abinsu amma sai ya sami wata yarinyar daban yaita soyayya da ita matsayin wadda zai aura alhalin ba aurenta zai ba, tana taya shi nishadi ne, in ma aka buncika ba ita kadai bace macen da yake kulawa ba, wanda yakewa hakan suna da yawa ita kuwa sauna kira mini sha-sha-sha in kaga sakarai ku tawo tare sai ta saki jikinta ta kori duk wasu samarinta masu sonta da gaskiya ta tare wajensa a nata tunanin aurenta zaiyi shi kuwa ko kusa ba shida niyyar kara aure yana tare da ita ne kawai dan taya shi hira da ci gaba da soyayyar da yayi lokacin kuriciya na saurayi da budurwa.
Za su ci gaba da soyayyar junansu ba tare data gane yaudararta yake ba koda kuwa wata ta kawo mata zancen abinda yake aikatawa ba zata yadda ba in kuwa zuciyarta ta fara amincewa da zantukan mutanen dake kawo mata magan-ganun da zarar ta sanar da shi zai kokarin kawar mata da zancen ya nuna mata sharri ne kawai irin nasu na mata koma ya shirya mata wata karyar kan cewa ai wadda ta fada mata sonsa take yaki amincewa shi ne ta biyo mata ta hakan, ita kuma sabida tsantsar son da take masa sai ta yarda da furucinsa a tsammaninta gaskiya ya fada mata wanda kuma ba haka bane.
Za su shafe tsawon shekaru ana soyayya amma a duk lokacin da akai maganar aure sai yace karta damu ita ce kadai matar da zai kara yaita dauke mata hankali har sai an gama aurar da kannen-kannenta ita tana zaune tana zaman jiran turowarsa be turo gidan su ba karshe gaskiya ta bayyana ya hau kame-kame na ba yadda zai, a lokacin zata gane yaudarar ta yayi.
Ku tara mako na gaba cikin wani sabon shafin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!