Connect with us

RAHOTANNI

Sojoji Sun Cafke Dan Boko Haram da Ake Nema Ruwa A Jallo

Published

on

Rundunar Sojojin Nijeriya, sun cafke daya daga cikin membobin kungiyar Boko Haram wanda rundunar ke nema ruwa a jallo. Rundunar sun cafke Babagana Abubakar wanda aka fi sani da Alagarno a Bulabulim Ngarnam dake garin Maiduguri.
Mai magana da yawun rundunar Sojin, Birgediya Janaral Sani Usman, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a. Inda sanarwar ta kara da cewa; sun kama Abubakar ne a lokacin da ya buya a wani daki dake cikin wani gida a yankin Bulabulim Ngarnam.
Usman, ya ce; daga cikin abubuwan da aka kama a maboyar dan ta’addan sun hada da; hulanan kwano, Katin dan kasa da katunan zabe, sannan akwai rigar wasanni, da kayayyakin Sojoji da sauran su.
Kukasheka ya tabbatar da cewa; tuni aka yi awon gaba da shi, domin ci gaba da gudanar da bincike. Ya tabbatar da cewa; rundunar Sojin ta 195, tare da ‘yan Sandan kwantar da tarzoma, da kuma ‘yan kato da gora na CJTF sune suka kama shi a jiya Alhamis.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!