Connect with us

SIYASA

Tsigaggen Mataimakin Shugaban PDP Ya Zama Daraktan Yakin Neman Zaben Gwamnan Bauchi

Published

on

Tsigaggen mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Babayo Garba Gamawa ya zama Daraktan yakin neman zaben gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar a karo na biyu.
A wata bayanin da Shamsudden Lukman mai taimaka wa gwamnan jihar Bauchi kan kafafen sadarwa ya sake, yana mai bayanin cewar Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar ya kaddamar da kwamitin yakin neman zabensa a karo na biyu tare da nada Alhaji Babayo Garba Gamawa a matsayin Daraktan yakin neman zabensa a karo na biyun.
Shi dai Babayo Gamawa, a ranar 7 ga watan nan ne jam’iyyar PDP ta fitar da wata sanarwar dakatar da shi daga ofis a matsayinsa na mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa a shiyyar Arewa, da zarginsa da yi wa jam’iyyar zagon kasa, jinkadan bayan fitar sanarwar ta PDP sai aka jiyosa da ganosa a fadar shugaban kasa yana bayanin sauya sheka daga cikin jam’iyyar PDP zuwa APC, lamarin da ya janyo kwanaki kalilan gwamnan APC a jihar Bauchi ya nadasa Daraktan yakin neman zabe.
Gwamna M.A dai ya nada kwamitocin ne a daren ranar Alhamsi a gidan gwamnatin jihar ta Bauchi da basu alhakin shiga kwararo-kwararo domin nemo masa kuri’u daga hanun masu yin zabe.
Shamsudden Lukman ya bayyana cewar gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abubakar shine ya zama shugaban majalisar bayar da shawara na yakin neman zaben nasa, inda mataimakinsa Audu Sule Katagum ya kasance mataimakin shugaban mai bayar da shawara na kwamitin yakin neman zaben.
“Alh. Babayo Garba Gamawa wanda shugaban kasa Muhammad Buhari ya karbe shi shekaran jiya a fadan gwamnatin tarayya da ke birnin tarayya Abuja a matsayin halartaccen dan jam’iyyar APC shine ya samu mukamin Daraktan yakin neman zaben Gwamnan, Muhammad Abdullahi Abubakar Esk a karo na biyu,” Inji Lukman
“Sauran jiga-jigan jam’iyyar PDP da suka kaura zuwa APC wanda suka hada da tsohon mataimakin Gwamnan jihar Bauchi a lokacin Ahmad Adamu Mu’azu wato Alhaji Abdulmalik Mahmood Barade Katagum da Alhaji Kaulaha Aliyu da sauran manyan jiga-jigai suna cikin wadanda suka samu halartan wannan taron,” Inji Lukman
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!