Connect with us

WASANNI

‘Yan Wasan Nijeriya Ba Su Da Zuciya

Published

on

Tsohon dan wasan Nijeriya na tawagar Super Eagles, kuma mai horar da ‘yan wasan kasar Tanzania a halin yanzu, Emmanuel Amunike, ya koka bisa gazawar da ‘yan wasan Najeriya ke yi wajen samun kyaututtukan hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar Afrika CAF.
A cewar Amunike ya kamata ‘yan Najeriya su farga cewa an shafe shekaru masu yawa basa samun kyakkyawan wakilci a duk lokacin da hukumar CAF ke gudanar da bukukuwan karrama ‘yan wasa, kungiyoyin kwallon kafa, da kuma masu horarwa a nahiyar Afrika.
Tsohon dan wasan na Super Eagles ya bayyana haka ne, yayin da yake tsokaci kan bikin bada kyautuka na hukumar ta CAF da ya gudana ranar Talata a birnin Dakar na kasar Senegal, inda Najeriya ta samu kyauta daya kawai, kyautar mafi kwazon tawagar kwallon kafa, tsakanin sauran takwarorinta na kasashen Afrika.
“Abin kunya ne ace har yanzu ‘yan wasan Najeriya sunki suyi hankali suyi tunani domin suna ganin ‘yan wasa daga kasashe daban-daban suna lashe kyautar gwarzon dan wasan Africa amma su ko a jikinsu” in ji Amunike
Yaci gaba da cewa “Najeriya tanada manyan ‘yan wasa a duniya manya manya da matasa kawai rashin mayar da hankalo ne da dagewa yasa basa tunanin samun wata kyauta wadda zata sake daga darajarsu data kasar su”
Nwankwo Kanu dai shi ne dan wasan Najeriya na karshe da ya samu nasarar lashe kyautar hukumar CAF ta gwarzon dan wasan kwallon kafar Nahiyar Afrika a shekarar 1999 kuma tun daga kansa babu wanda ya sake lashewa
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!