Connect with us

RAHOTANNI

Za Mu Ci Gaba Da Tsaro Wakokin Da Za Su Ci gaba Da Mara Wa Jam’iyyar APC

Published

on

Ma’ajin kungiyar mawakan Hausa masu yima jam’iyyar APC waka Isyaku Muhammad Boris ya bayyana cewar kungiyarsu za ta ci gaba da tsaro wakokin da za su ci gaba da taimaka wa jam’iyyar APC a wajen samun nasarar lashe zabuka masu zuwa na shekarar 2019 da ke tafe a duk fadin kasar nan.
Ma’ajin kungiyare mawakan Hausan ya yi wannan ta’aliki ne a garin Malumfashi jim kadan bayan kammala zagaye tare da neman samun kuriar talakawa a yankin Funtuwa. Ya ci gaba da cewa jam’iyyar APC jam’iyya ce ta talakawa kuma aka ginata a cikin adalci wajen yi wa al’uma ayyukan raya kasa da kare hakkokinsu.
A kan haka ne kungiyrsu ta mawakan siyasa suka ga ya kamata suma su ci gaba da ba da ta su gudummowar domin jam’iyyar APC ta kara samun ci gaba tare da samun nasarorin lashe zabuka masu zuwa na shekarar dubu biyu da goma shatara.
Sannan ya ci gaba yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a kokarinsa na ciyar da kasar nan gaba tare da kawo ayyukan Alheri da al’umar Nijeriya za su ci gaba da amfana.
Ya kara da cewa, haka shi ma Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya taka rawar gani a jihar katsina wajan kawo tsaro da kiwon lafiya da ilimin zamani da ruwan Sha da kuma wutar lantarki in ji sh. A kan wadannan abubuwa na ci gaba al’uma yake bukaci al’ummar jihar Katsina da Nijeriya baki daya da su ci gaba da ba wadannan mutane hadin kai da goyan Baya mussamman a lokacin zabe mai zuwa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!