Connect with us

RAHOTANNI

An Kaddamar Da Littafin Ilimin Rubutun Labari Na ‘Turbar Addini Da Al’ada’

Published

on

Bayan samun nasarar kammala aikin wallafawa da kuma bugawa, tsugunne ba ta kare ba, saboda batun kaddamar da wannan mashahuran ayyuka.
Kamar dai yadda aka sani cewa, yana da matukar wahala a iya cimma wani abu mai muhimmanci ba tare da an fuskanci kalubale da wahalhalu ba. Nan dai a ka shiga zirga-zirga. Marubucin, Hashim Abdallah shi da mataimakansa suka dukufa don ganin dai an cimma wannan gagarumin aikin kaddamarwa da aka faro. Aka buga nan, aka buga can, yau ne, gobe ne, har dai al’amarin kaddamar da littatafan biyu ya je gaban fitaccen dan kasuwar nan, ginshiki a Jigawa, wato mamallakin kamfanin gine-gine da aikin hanyoyi da ake kira Gerawa Global Construction Company, wato, Alhaji Isah Muhammad Gerawa, wanda ya yi murna, cike da walwala ya karbi tayin kasancewa babban mai kaddamarwa. A yayin da ya kara da cewa wannan wani gaggarumin al’amari ne da ya shafi ilimi, don haka, ba za mu yi wasa da shi ba, za mu kaddamar da wadannan littattafai a ranar juma’a mai zuwa, wato 29 ga watan Disambar shekarar 2018 kamar yadda aka yi abin kuma ya gabata.
Alhaji Isah ya sanya wannan ranar ne bisa la’akari da muhimmancin wadannan littattafai. Haka kuma, in aka yi la’akari da tarin uzurirrikan da ke gaban attajirin dan kasuwar, ba mamaki don ya sa a wata rana da yake ganin zai fi samun dama.
Cikin ikon Allah, kurarren lokacin dai bai hana bikin kaddamarwar armashi da tasiri ba ko kadan.
Sai ma sanya wannan rana ya faranta ran ‘yan kwamiti da kungiyar marubutan masarautar Hadejia, wadanda suka yi fata kuma suka ci alwashin cewa, da yardar ba za su bari a tsallake shekarar 2018 ba tare da an gudanar da bikin ba.
Sakamakon haka, aka tsara gudanar da wannan biki a wannan rana ta juma’a cikin kwanaki biyu kacal a garin Malam-madorin jihar Jigawan Najeriya, kana, Alhaji Isah Gerawa ya zamo babban mai kaddamarwa a yayin taron, har ma ya sayi littattafan, kuma ya biya kudin a nan take.
Wani gaggarumin abu da ya taimaka wajen tumbatsar wannan muhimmin taro shi ne, shi da kansa, wannan gogaggen dan gwagwarmayar da ya taba shugabantar kungiyar ‘yan jaridu ta Najeriya reshen jihar Jigawa har sau biyu, wato kwamared Fahad Muhammad shi ne mai gabatarwa a gurin wannan taron.
Fasihin masanin lakantar ilimin kimiyyar takarar Alkur’ani mai girma, kuma shugaban sashen ilimin kimiyyar Alkur’ani na kwalejin karantar Musulunci da shari’a da ke garin Ringim, Dr Dahir Adam Ibrahim shi ne ya jagoranci bude taro da addu’a.
Sa’annan, mataimakin shugaban jami’ar karatu-daga-gida ta jihar Jigawa, Farfesa Abdullahi Doguwa, ya gabatar da takaitaccen sharhi da bayanan sirrika da ilimi da irin saukakan hanyoyin koyo da sanin ka’idojin harshen Turanci bangaren furuci daga littafin Simplified English Pronunciation.
Haka zalika, Dr. Lawan Danzomo na sashen karatun Turanci da al’amuran adabi na jami’ar Bayero da ke Kano, ya yi fashin-baki gami da karin haske da fa’idar wadannan littattafai, kana ya zaburar da marubucin da ya kara kaimi da fadada irin wannan littafin furuci.
Shi kuma Dr. Auwalu Ado Aujara na kwalejin karatun Arabiyya da harkokin Shari’a da ke garin Ringim a jihar Jigawa, kuma fitaccen masanin ilimin adabi da bunkasa al’adu, ya hikaito tasiri da irin rawar burgewar da littafin Ilimin Rubutun Labari Cikin Adabi (Turbar Addini da Al’ada) zai iya takawa wajen sharewa mai karatu hanya tare da matso masa nesa kusa har ma ya zamewa mutum kurangar da zai taka ya kai ga matsayin fahimta da sani da samun ilimin ka’idoji da hanyoyin da mutum zai bi ya yi fintinkau, ya zamo gagara-gasa a fannin kagar labarai masu ma’ana da fa’ida da azanci da hikima da gargadi da debe-kewa, kuma ba tare da an sauka daga kan koyarwar addini ko al’ada ba.
Daga cikin ababen gata da karramawar da wannan biki ya yi katarin samu, wadanda suka karo armashinsa, har da kasancewar tsohon ministan wutar lantarki da tama da karafa, Ambasada Ahmad Abdlhamid a matsayin shugban wannan gagarumin taro.
Duka dai cikin shaukin farincikin samun wannan hazikin mawallafin a jihar Jigawa mai albarka, da murnar samun wadannan littattafai da za su saukaka mana hanyoyin koyon furucin Turanci da iya kago labarai cikin harshen Hausa.
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa, Ahmad Mahmud Gumel, wanda shi ne shugaban yakin zaben APC na Jigawa a 2019, wanda har ila yau kuma ya wakilci gwamnan jiha, Alh. Badaru Muhammad Abubakar a yayin wannan taro, ya sayi nasa kwafin kuma shi din ne ya fansa wa mai girma gwamna.
Daga cikin mashahurai kuma dimbin mutane masu muhimmancin da suka halarci wannan biki, akwai kwamishinan Shari’a na jihar Jigawa, Barista Sani Hussaini Garin Gabas, wanda bayan ya fanshi nasa littattafan, sai kuma ya dada da yin alkawarin bayar da kariyar shari’a kyauta ga mawallafi Hashim Abdallah ko da bukatar hakan na iya tasowa.
Har ila yau, Barista Modibbo ‘Yelleman, wanda malami ne mai koyar da sashen shari’a, yana cikin wadanda ba su yi kasa a gwiwa wajen halartar wannan taro ba.
Fitaccen mawallafi kuma babban dillalin saye da sayar da littattafan Hausa, shugaban madaba’ar littattafai mai suna GBS Bookshop, wato Nasir Garba Muhd, shi ma ya halarci wannan gagarumin taro. Baya da shi, akwai mawallafin littattafan Hausan, Bello Muhd Bello Ringim, tare da masanin tarihin nan wato Sulaiman Ginsau Hadejia da dan jarida mai zaman kansa, Matashi Abdullahi Hadejia da kwararren marubucin kafar sada zumunta ta zamani Auwal Tahir Sabon Gida, (Mai Tandun Kauna) gami da marubucin shirin nan na gidan talabijin din ARTB Kano mai dogon zango (series film mai taken INDA BA KASA… wato Jazuli Ya’u Hashim da sauran marubuta labarai irin su Abdul’aziz Liman. Akwai kuma irin su Sagir Al-jazariy wanda ya yi takakka tun daga Kaduna, duk kuwa da kurarran lokacin domin halartar wannan biki.
Mutane masu tarin yawa, musamman daga garin Malam-madori sun yi tururuwar halartar wannan gagarumin taro na kaddamar da wadannan littattafai da dan’uwansu Hashim Abdallah ya wallafa gami da jin dadi da alfaharin wannan abin-kai da suka samu a cikin garinsu.
Daga karshe, Limamin Babban Masallacin Juma’a na garin Malam-madori, Sheikh Umar Ya’u Hashim ne ya jagoranci rufe wannan taro da addu’a.
Rahoto daga Ayuba Sani Namakka na gidan talabijin ta Jigawa, Jigawa Telebision, JTb.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!