Connect with us

LABARAI

Babu Adalci A Gwamnatin Buhari – Tambuwal

Published

on

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewar abubuwan da ke faruwa a Nijeriya ba Dimokuradiyya ba ce ba kuma jagoranci ba ne illa yaudara don haka ya yi kira ga al’umma da su zabi jam’iyyar PDP domin samun kyakkyawan shugabanci.
Tambuwal ya bayyana cewar gaskiya, adalci da rikon amana da Gwamnatin Muhammadu ke ikirari a baki ne kawai ba tare da aiwatar da hakan a zahiri ba kamar yadda ‘yan Nijeriya suka yi tsammani.
Gwamnan ya bayyana cewar akan wannan ne suka sauya jam’iyya kuma yana da tabbacin da yardar Allah jam’iyyarsa ta PDP za ta lashe dukkanin zaben 2019 daga sama har kasa bakidaya.
Tambuwal ya bayyana hakan ne a yayin da yake yi wa magoya bayansa jawabi a gangamin yakin neman zaben PDP na Yankin Gabascin Sakkwato a Karamar Hukumar Wurno.
“Ina kira gare mu Sakkwatawa mu sani wancan dodon bango da ake yi cewar wai wane yana da gaskiya, to idan yana da gaskiya ya kama Mamman Daura da Abba Kyari mana ya yi masu hukuncin abin da suka aikata. Amma ba zai kama su ba sai dai ya kamata Sanata Goodswill Akpabio domin a tursasa masa komawa APC, wanda a yanzu da ya riga ya koma jam’iyyarsu ya zama wankakke maras datti.” In ji Gwamnan.
Ya ce duk wanda aka gani yana da karfin zuciya ko magoya baya idan ba Allah ya kiyaye shi ba sai a bashi tsoro. “Shi kansa o’o (Sanata Aliyu Wamakko) tsoro a ka bashi na cewar EFCC za ta kama shi, shi yasa ya guji inda ya kamata ya tsaya domin mu ci-gaba da taimakon al’umma. Da macijin ragga ba ma macijin kwarai aka bashi tsoro ba, mu kuma ba mu tsoron kowa sai Allah domin gaskiya muka sa a gaba ba mu da niyyar zalunci ko gurabata tarbiyar matasa.” Ya bayyana.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya kuma yi alkawalin ci-gaba da gudanar da ayyuka masu yawa a Sakkwato ta hanyar gine-gine, aikin gona, kiyon lafiya, ilimi da tallafawa al’umma idan aka sake zaben shi a karo na biyu. Ya ce wadannan ayyuka ne da ya yi kuma zai ci-gaba da yi domin bunkasa Jihar Sakkwato da inganta rayuwar al’umma tare da inganta tarbiyar matasa.
A jawabinsa Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Attahiru Dalhatu Bafarawa ya yi kira ga al’ummar jihar da su zabi Tambuwal a matsayin Gwamna a karo na biyu tare da bayar da cikakken goyon baya ga dukkanin ‘yan takarar jam’iyyar domin samun kyakkyawan shugabanci.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!