Connect with us

RIGAR 'YANCI

Barin Shekarau PDP Ta Sa Mu Ka Hakura Da Takara A APC –Hon. Sada

Published

on

Daya daga cikin ’yan tarakar majalisar tarayya a karamar hukumar Nasarawa, HON. AUWALU ABBA SADA na jam’iyyar PDP kafin su canja sheka tare da tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Malam Ibirahim Shekarau ya bayyana wa wakilin LEADERSHIP A YAU LAHADI, HARUNA AKARADA, cewa, ficewar tsohon gwamnan daga cikin jam’iyyar ta PDP ne ya assasa su ka bar ta kuma su ka bi shi zuwa jam’iyyar da ya koma ta APC, inda Sardaunan na Kano ya ke yin takarar kujerar sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya. Ga dai yadda hirar ta kasance:

Ka na daya daga cikin na gaba–gaba a wajen Sardaunan Kano Dr. Malam Ibirahim Shekarau, kuma ka na daya daga cikin ’yan takara a PDP kuma ga shi kun koma jam’iyyar AP C. Ya ya za ka yi da yunkurinka na takara?
To, da ma wannan takara da mu ka tsaya ’yan uwa ne da abokan arziki su ka same ni, domin na fito wannan takara. To, kasancewar mu siyasarmu ta bangaren mai girma Sardaunan Kano ta sa mu ka fito a wannan locacin, mun dade mu na wannan gwagwarmaya domin mu wakilci karamar hukumar Nassarawa a matakin tarayya, to kuma an yi ta yin gwagwarmaya. To wani yanayi ga shi ya sa mun dawo jam’iyyar APC kuma mu na bada gudunmawarmu a tafiyar Malam Ibirahim Shekarau, kuma sanata wanda zai wakilci Kano ta tsakiya.

Ga shi kun yi takara a wancan lokaci, to, yanzu yaya za a yi?
To, da ma mun fito ne takara domin mu kawo chanji, kuma mu nuna wa mutane wainar da a ke toyawa a zauren majalisa na kasa. Wannan shi ne dalilin da ya sa mu ka fito. Allah cikin ikonsa mu ka samu kanmu a wannan jam’iyya. Don haka ba lallai ne mu fito ba, saboda yanzu ne mu ka shigo, sai dai za mu cigaba da marawa Sardaunan Kano baya har sai mun ga ya zama sanatan Kano kuma mu na kara duba ga yanayin da mu ka tsinci kanmu, amma ba ma danasanin komawarmu APC. Don haka aikin da ke gabanmu shi ne tabbatar da Malam Ibirahim Shekarau ya zama sanatan Kano ta Tsakiya. Hakan zai nunawa duniya cewa ya yi kokari, domin zuwansa zauren majalisa zai kawo canji da dama sakamakon wanda ya ke kai ya gaza.

To, mene ne kiranka ga jama’a?
Kirana shi ne mu tashi mu mike tsaye wajen yakar zalunci, shi ne zai tabbatar ma na cewa za a samu canji a kasar nan. Kuma shi Malam kowa ya san abinda ya yi na tallafa wa al’umma da kuma kawo ayyuka. Mu na da tabbacin cewa a wannan gabar ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen kawo ayyuka daban–daban. A matsayinmu na wadanda mu ke kusa da shi, akwai shawara da za mu cigaba da kawowa, saboda a tallafa wa mutane. Wannan shi ne abinda mutane za su gani a 2019 izuwa 2023.

Wanne kira ka ke ga al’ummar Najeriya a kan zabe mai zuwa?
To ka san tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonaton, ya ce, babu wata gwamnati da za ta kawo canji a shekara hudu. Gwamnatin Muhammadu Buhari ta na iya kokarinta wajen kawo canji, don ganin cewa an dawo wa da Najeriya martabarta. To, mu na kara fada wa jama’a cewa su ba wa shugaban kasa da gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje kuri’a a 2019, domin a samu habakar tattalin arziki, domin yanzu kokarin da a ke yi kenan.

Wanne kira za ku yi ga wadanda ku ka bari a PDP wajden su dawo ku cigaba da tafiya tare?
To, gaskiya ba mun bar jam’iyyar PDP haka kawai ba, a’a, face saboda rashin adalci da shugabanci na kasa ya yi ma na na rushe shugabancin jihar Kano da ma sauransu. Don haka mun bar PDP ne saboda rashin adalci. Don haka ga wadanda su ka zauna a cikin jam’iyyar, kada su yi tunanin za a yi mu su adalci, saboda shi adalci abu guda daya ne. Idan ka ga abinda ya dace ka yi, to ka yi. Idan ka ga abinda bai dace ba, kada ka yi. Mu na ba su shawara da su taho mu dinke a jam’iyyar APC mu ciyar da jama’ar Kano da kasar nan bakidaya gaba.

Ga shi dan karamar hukumar Nassarawa kuma tsohon ciyaman kuma kwamishinan gona, Alhaji Nasiru Gawuna, ya zama mataimakin gwamnan jihar Kano? Me za ka ce kan hakan?
Gaskiya nasara ce wacce ba za ta misalltu ba. Na farko dai mu na yiwa Allah godiya da ya bai wa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna wannan matsayin, domin mu a ka yi wa babu. Abinda zan ce da mai girma gwamnan jihar Kano godiya ta musamman ce, saboda a duk fadin Kano sai a ka zabi karamar hukumar Nasarawa a ka ba mu wannan matsayin, abu ne wanda ya ke duk wani dan karamar hukumar Nassarawa dole ya yi godiya da wannan kyauta da ta samu ’yan yankin karamar hukumar.

Mun gode.
Ni ma na gode. Allah dai ya saka da alheri.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!