Connect with us

WASANNI

Bayern Munchen Za Ta Daukaka Kara A Kan Muller

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta ce za ta daukaka kara kan dakatarwar wasanni biyu karkashin gasar cin kofin zakarun Turai da aka yi wa dan wasanta na gabaThomas Mueller dan kasar Jamus.
Dakatarwar kan Mueller dan Jamus mai shekaru 29 na nuni da cewa ba zai samu damar buga wasa a wasanni biyu na zagayen kungiyoyin 16 da Bayern Munich din za ta faffata da Liverpool ba.
Tun a wasan karshe na zagayen rukuni rukuni ne UEFA ta fitar da Mueller daga filin wasa bayan bashi jan kati a wasan wanda aka yi canjaras tsakanin Munich da Ajad kwallaye 3 da 3 kafin daga bisani ta sanar da dakatar da shi daga buga wasanni biyu bayan tabbatar da cewa da gayya ya hankade tare da dukan dan wasan gaba na Ajad Nicolas Tagliafico.
Sai dai kungiyar Bayern Munchen ya ce ko da dakatarwar za ta yi amfani bai kamata ta zamo a ilahirin wasanninsu biyu da Liverpool ba, wasan da lallai suna bukatar nasara don tsallakawa mataki na gaba.
A ranar 19 ga watan Afrilu ne dai Bayern Munich za ta yi tattaki zuwa filin wasa na Anfield kafin daga bisani ita ma Liverpool ta je Allianz Arena a ranar 13 ga watan Maris din domin buga wasa na biyu.
A cewar Bayern Munchen tana fata ko da Mueller bai samu wasan da za su yi tattaki zuwa Liverpool ba amma ya zama ya samu zarafin buga wasa a wasan da Liverpool za ta zo musu har gida cikin watan Maris.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!