Connect with us

WASANNI

Har Yanzu Ronaldo Ya Na Cikin Rikici

Published

on

‘Yan sanda a birnin Las Begas na kasar Amurka sun bukaci a ba su kwayoyyin halittar (DNA) na shahararren dan wasan kwallon kafar nan, Cristiano Ronaldo, domin gudanar da bincike a kan zargin da ake yi masa na aikata fyade.
Lauyan dan kwallon Peter S. Christiansen ya shaida wa manema labarai cewa bukatar kawo kwayoyyin hallita ba sabon abu bane kuma Jaridar Wall Street Journal ta wallafa cewa an aika takardar bukatar hakan ne zuwa wata kotu da ke kasar Italy.
Sai dai Ronaldo ya musanta zargin da ake masa na cin zarafin Kathryn Mayorga a wani otel da ke Las Begas a shekara ta 2009 wato shekarar daya canja sheka daga Manchester United zuwa Real Madrid.
Lauyan dan kwallon ya bayyana cewa “Har yanzu Ronaldo yana kan bakarsa, abin da ya faru a Las Begas a 2009, ba fyade ba ne, da amincewar ta, ba abin mamaki ba ne idan an ga kwayoyin halittar Ronaldo ko kuma ‘yan sanda su nemi kwayoyyin domin bincike.’’
Mujallar Der Spiegel ta kasar Jamus ce ta fara wallafa zargin da Ms Mayorga ta yi, bayan ta kai kararsa wajen ‘yan sanda a Las Begas bayan faruwar lamarin kuma mujallar ta bayyana cewa a shekarar 2010, Ms Mayorga ta yi wata yarjejeniyar sirri da Ronaldo a kan ya biyata dala 375,000 domin kada ta tona masa asiri.
Lauyan Ronaldo dai a baya ya bayyana cewa wanda yake karewa bai musanta yin wannan yarjejeinyar sirrin ba sannan ya kara bayyana cewa “wannan yarjejeniyar ba wai tana nuni da Ronaldo ya aikata abin da ake zarginsa da shi ba ne.”
Lauyan Ms Mayorga ya bayyana cewa wata kungiya ta #Metoo Mobement ce ta jawo ra’ayin Ms Mayorga da ta fito ta bayyana abin da ya faru, inda yanzu haka ta yi karar Ronaldo a Amurka.
Ronaldo dai ya koma kungiyar kwallon kafa ta Juventus daga Real Madrid a kan fam miliyan 99.2 kuma ya ci kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Ballon d’Or a 2008, 2013, 2014, 2016 da kuma 2017.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!