Connect with us

DAGA TEBURIN EDITA

Kannywood: Shin Su Waye Su Ka Fi Yin Nasara A Sinimar Zamani?

Published

on

A ’yan shekarun nan masu shirya finafinai a masana’antar Kannywood sun fi mayar da kai ga kai finafinansu a sinimar nan ta zamani da ke Ado Bayero Mall a birnin Kano, maimakon sakin finafinan barkatai a kasuwa kamar cinikin gyada. Hakan ya bude wata sabuwar kasuwa da tserereniya tsakanin masu sana’ar, don tabbatar da samun karbuwar sababbin finafinan da su ka shirya. Wannan tsere ya sake bude shafin yin nazari da bincike kan ko su waye su ka fi samun nasara tun daga lokacin da akalar kasuwar fim din ta fara koma wa sinimar, wacce a ke kira da Film House Cinema da ke Kano.
Ganin cewa, shekarar 2018 ta kare, sannan kuma a na farkon shekarar 2019, LEADERSHIP A YAU LAHADI ta gudanar da wani kwarya-kwaryar bincike, don gano mu ku gaskiyar wadanda su ka fi samun nasara a sabuwar kasuwar ’yan fim din. Ga jerin abinda bincikenmu ya nuna da kuma wasu daga cikin dalilai:

Daraktan Da Ya Fi Samun Nasara: Ali Nuhu
Fim Din Da Ya Fi Samun Nasara: Ruwan Dare
Furodusan Da Ya Fi Samun Nasara: Abubakar Bashir Maishadda
Jarumin Da Ya Fi Samun Nasara: Adam A. Zango

Darakta Ali Nuhu:
Nasarar da a ke nufi fitaccen tauraro Ali Nuhu ya samu a sinimar Film House ba a matsayinsa na jarumi ya same ta ba, a’a, ya same ta ne a matsayinsa na darakta, domin babu daraktan da finafinansa su ka fi karbu wa a sinimar kamar nasa. Shi ne ya bayar da umarni a finafinan da a ke ganin sun fi kowadanne finafinai karbu wa a wannan sinimar ta zamani, wato Mansoor, Mariya da Mujadala. Babban abin jan hankali a nan shi ne, gabadayansu ba shi ne ya jagorance su ba a matsayin babban tauraron shirin (wato Leading Character). Ya mayar da hankali ne kan aikin bada umarnin sosai, inda ya fito a matsayin mai taimaka wa jaruman kawai.
Babu wani darakta da ya ke da finafinai uku rigis wadanda su ka karbu su ka kuma yi tasiri a sinimar har ’yan kallo su ka yi tururuwar zuwa su kalla, sai Darakta Ali Nuhu.
Da wannan LEADERSHIP A YAU LAHADI ta ke ganin ya cancanci a kira shi a nada matsayin darakta mafi samun nasara a sinimar zamani ta Film House a Kanywood.

Fim Din Ruwan Dare:


Mun san da yawa za su yi mamakin ganin fim din Ruwan Dare a matsayin fim mafi samun nasara a sinimar zamani ta Film House da ke Ado Bayero Mall a Kano. To, ba mu zabi fim din Ruwan Dare ba, don ya fi kowanne fim karbuwa, tabbas akwai finafinai da su ka fi shi karbuwa a sinimar, amma sai dai wasu muhimman abubuwa da fim din ya hada su ne su ka saka ya zama fim mafi samun nasara a sinimar tun kawo yanzu tun bayan kafuwar wannan sabuwar kasuwar. Fim ne wanda yawacin masu kallon da su ka shiga su ka kalle, idan sun fito su na gamsuwa da cewa, ba su yi asarar kudinsu ba, saboda ma’anar da ya yi da kuma gamsarwar da ya ke yiwa ’yan kallon. Duk inda cikakken Bahaushe ya ke a duniya, zai iya gamsu wa da cewa, an wakilce shi a cikin Ruwan Dare. Za a iya cewa, gamsuwar da fim din ya bayar ce ta sa sau biyu gidan sinimar su na kara ma sa kwanakin lokacin haska shi bayan wa’adin lokaci na farko ya kare.
Bugu da kari, a cikin fim din Ruwan Dare babu fitattun jaruman da a ka fi camfa wa da cewa, sai da su fim ya ke karbuwa a Kannywood, wato Ali Nuhu da Adam A. Zango. Ba a na nufin jaruman fim din ba fitattu ba ne, amma dai ba a camfa su ba. Jarumai ne wadanda a ka fi yarda da kwarewarsu fiye da tashensu. Haka nan daraktan fim din ba Aminu Saira ba ne, ballantana a ce sunansa zai iya taimaka wa fim din. Kawai abinda za ka iya cewa shi ne, daraktan Ruwan Dare, wato Yasin Auwal, da ma a sinimar shi ba bako ba ne, domin shi ne ya taba kawo fim din Rariya, wanda shi ma ya yi matukar samun nasara a sinimar. Don haka za a iya cewa, da ma daraktan ya na gaba da Saira a sinimar, duk da cewa shi za a iya yi ma sa uzurin cewa, har kawo yanzu bai taba kai fim sinimar ba ballantana a yi gaggawar yanke ma sa hukunci. Baya ga haka kuma kamfanin da ya dauki nauyin shirya Ruwan Dare, ba UK Entertainment ba ne, bare wani ya ce da ma kamfanin ya saba shirya finafinai ingantattu, karbabbu kuma masu tashe. Yamsa Multimedia ne su ka shirya fim din na Ruwan Dare.
Wata babbar nasarar da Ruwan Dare ya samu ita ce, duk da karbuwar da ya yi, amma ba a nuna shi a lokacin da a ka fi shiga kallon finafinai ba, wato lokutan bukukuwan salla ko karshen shekara, wadanda lokuta ne mutane su ka fi samun hutu ta yadda za su fi samun sukunin zuwa gidan sinima su yi kallo da nishadi. Kuma shi ne fim na farko da ya fara karbu wa a lokacin da ba na biki ko hutun komai ba.
Bisa dogaro da wadannan hujjoji LEADERSHIP A YAU LAHADI na da ra’ayin cewa, fim din Ruwan Dare shi ne fim mafi samun nasara a sinimar Film House da ke Kannywood.

Furodusa Abubakar Bashir Maishadda:
Kawo yanzu babu wani furodusa da ya kai finafinai har guda biyar a sinimar zamani ta fim Film House Cinma da ke Kano kuma su ka kai matakin karbuwa kamar Furodusa Abubakar Bashir Maishadda. Shi ne ya kawo fitattun finafinan nan na Kalen Dangi, Mariya, Mujadala da kuma wadanda a ka dauka da harshen Turanci guda biyu, wato This Is The Way da In Search Of The King. Wadannan finafinai guda biyu da mu ka ambata na Turanci su ne kadai finafinan da a ka shirya da yaren da ba na Hausa ba a Kannywood kuma a ka gwada kai su sinima. Wannan ma abin alfahari ga wannan zakakurin mai shiryawa.
Finafinai guda biyar a jere ba tare da samun wani babban tasgaro ba, ba karamar nasara ba ce ga Furodusa Maishadda. Don haka LEADERSHIP A YAU LAHADI na da ra’ayin cewa, da wadannan hujjoji za a iya cewa, kawo yanzu Furodusa Maishadda shi ne mai shirya finafinan Hausa mafi samun nasara a sinimar zamani ta Film House da ka Kannywood.

Jarumi Adam A. Zango


A fili ta ke cewa, Jarumi Adam A. Zango ya fi kowanne jarumi samun karbu wa a wannan sinima ta zamani mai suna Film House da ke Ado Bayero Mall a birnin Kano. Za a iya cewa, fim din da ya jagoranta na Gwaska The Return shi ne kafa harsashin yin tururuwa a kalli finafinan Hausa a wannan sinimar, domin bincike ya nuna cewa, ba a taba samun fim din da masu kallo su ka cika dukkan dakunan sinimar Film House kusan guda shida ba, sai a lokacin da masu kalo su ka je kallon jarumin a matsayin Gwaska. Kuma Adam Zango shi ne kadai jarumin da yara da matasa su ka taba kwaikwaya tun bayan kallon wannan fim na Gwaska, wanda ya ke saka fuskar bad-da-bami a ciki. Hakan ya sanya yin tururuwa a lokacin nuna Gwaska The Return ba don ainihin fim din ba, illa don kawai shi jarumin fim din.
A takaice ma dai, bincikenmu ya nuna cewa, da yawa su na tsammanin fim din ya fito kasuwa, amma alhali gaskiyar managa ita ce ba a sake shi a kasuwa kaset ba har kawo yanzu, illa dai tun kallon da a ka yi ma sa a sinima kuma a ke cigaba da zaman tsammanin warabbukan fitowarsa. Wani binciken ya nuna cewa, da za a sake dawo da fim sinimar, to akwai yiwuwar ’yan kallo za su sake koma wa su kalli jarumin.
Da irin wadannan hujjoji ne LEADERSHIP A YAU LAHADI ke da ra’ayin ganin cewa, Jarumi Adam Zango shi ne jarumi mafi karbu wa a sinimar Film House da ke Kannywood.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!