Connect with us

SIYASA

Karya A Ka Shirya Amma Lafiyata Garau, In Ji Tinubu

Published

on

Daya daga cikin shugabanin APC na kasa, Bola Tinubu, a jiya ne yake karyata rahotonnin da suke yawo na cewar an garzaya da shi asibiti bayan kwasan jiki da ya yi ya fadi.
Da yake bayani a jiya a Abuja a lokacin da ya amshi bakwancin wakilan shugabanin Sarakunan gargajiya a shiyya Kudu Maso Yamma a karkashin jagorancin Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi.
Bola Tinubu ya yi fatali da labarin da ke cewa an garzaya da shi asibiti ruwa-ruwa, ya ce bayani ne kawai aka fitar daidai da labara marar tushe.
Tinubu, dai wanda ke bayani kan rashin ganin duriyarsa a taron ganawa na gwamnoni kan yakin neman zaben shugaban kasa, ya nuna bayanin da cewar labarin kanzon kurege ne kawai.
Ya ce rashin ganinsa a wajen taron gwamnonin bai rasa nasaba da tsarin siyasa, ya bayyana cewar ba komai ne za su ke sa kansu a lokaci guda ba, don haka ne ya yi nuna da cewar dole ne a wasu lokutan gwamnonin suke tattauna abun da ya shafesu daidai da jahohinsu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!