Connect with us

DAGA TEBURIN EDITA

Mafi Yawan ’Yan Kannywood Buhari Su Ke Yi – Iliyasu Abdulmumin Dankasa

Published

on

Kusan za a iya cewa babu wani lokaci da ’yan fim ne masana’antar finafinai ta Kannywood suka fi shiga harkokin siyasa kamar wannan lokacin domin kuwa da wuya ka samu wani dan fim din Hausa da ba ya siyasa. ILIYASU ABDULMUMIN, wanda a yanzu aka fi sani da ‘DANKASA’ ya na daya daga cikin wadanda suke gaba a cikin harkar siyasa, don haka ne muka ji ta bakinsa a game da shigar ‘yan fi harkar siyasa da kuma shirinsa da ya ke yi a soshiyal midiya mai suna Dankasa.

A matsayinka na tsohon jarumi a cikin harkar fim kuma mai ba da umarni ko me za ka fada game da yadda kuka shiga harkar siyasa a wannan lokacin fiye da yadda aka san ku a baya?
To, ka san kowa da iri fahimtarsa kuma kowa da irin hanganes.a to ni a tawa mahangar akwai wasu dalilai biyu zuwa uku wadanda suka sa ‘yan fim suka shiga siyasa. Na farko karyewar tattalin arziki wanda ya taba kasuwanni har ma da na fim. Ya zama babu aiki sosai kamar yadda ake yi a baya. A biyu kuma akwai wani abu da ‘yan siyasa suke yi na fada ba cikawa. An yi mana alkawaruka da yawa baya idan aka ci mulki ba a kara waiwayarmu. Sai lokacin da siyasa ta dawo. Bayan kuma duk wani ilimi da gogewa da ake nema to akwai masu irinsa a cikin ‘yan fim, amma sai mu zura idanu muna kallo don haka tun daka fara siyasa ita masana’antar tana nan jiya kamar yau, domin kuwa babu wani canji da aka samu na canji da gwamnatin siyasa ta kawo mana wanda za mu ce ga shi yau mun gani a kasa a maimakon haka ma sai dai a a zo mana da bain da zai rinka jawo mana tsinuwa. To wadannan su ne dalilan da suka sa sa kuma ra’ayi domin shi dan fim ne kamar kowa. Kuma duk duniya babu wata masana’antar fim da ba ta siyas,a domin ana yin amfani da ‘yan fim a yada manufa ta siyasa, mune a nan ma ba a yin hakan to kuma sai a yanzu wani abu ya zo a tsakanin fari da baki, don haka ni yanzu ina yin fim to kuma ina makomar ‘ya’yana da suke tasowa? Don haka dole ne na gane ba da tawa gudunmawar don ganin an samu kasa ingantacciya. Don haka da ni da sauran yan fi muna da wannan hakkin yin siyasa ta ra’ayin kanmu.

To a zabe 2015 kusan ‘yan fim daya a siyasa APC suka yi amma a yanzu ana ganin kowa ya kama gabansa.
To ina ganin ko a gidan ka ne ana samun mabanbancin ra’ayi, don haka halitta ce ta dan adam ba zai yiwu a taru a zama daya ba, amma dai na san mafi yawan ‘yan fim da ba sa APC wadansu ne da aka batawa idan yanzu na tafi na ga gwanina kuma ban je da kai ba kuma kai ma kana ra’ayinsa to haushi za ka ji. To sai mutum ya ce unda a a yi da ni bari na karkata na yi wani wajen. To ita kuma harkar fim masu kallo ba su sani ba domin wata harka ce da take da gasa. Duk lokacin da wani ya yunkuro ya yi wani abu to waus za su yi kokairn su ga sun yi irin wannan. To ganin an yunkuro an karkata wajen Shugaban kasa mai ci a yanzu sai ya sa wadnada ba su samu dama sun yi tafiyar ba suke ganin ya za a bar su a kasa? To bari su ma su yi wani wajen. Amma dai abin da nake so ka gane mu inuwarmu daya kuma har ga Allah mafi yawan ‘yan fim a cikin zuciyarsu Buhari suke yi.

A kwanan nan ana ganin ka a sohiyal mediya cikin wata kuma da sunan dankasa kana tallan Buhari ko wane ne ya dauki nauyinka?
To ni dai wannan da kaina na yi ina yi ne a matsayin nawa tallafin ga shugaban kas amai ci a yanzu kuma wani abu da mutane ba su sani ba, ni ba a yanzu nake kaunar Buhari ba, don tun lokacin da ya gama aikinsa a PTF mutane suna kai masa hari a kan ya fito siyasa yana cewa ba zai yi ba, don akwai wani Sani Uba a Daura a karkashin ofishina yake a nan Kano mawaki ne, to akwai lokacin da muka tsara waka muka tafi Daura har gidan Buhari muka kai masa wakar muka nuna goyon bayanmu a gare shi ya ce ya gode amma dai siyasa ba shi da ra’ayi a wannan lokacin. To ka ga ba wani abu ne sabo a gare ni ba don haka a yanzu nake ganin wacce gudunmawa zan a shi sbaoda wani kuskure ne yake nema ya faru a kasar nan da ni a mahangata nake gani kuskure ne domin idan utum ya duba sai ya ga mene ne ya fari a mulkin baya, kuma me ya faru a yanzu don haka sia ka yi alkalanci idan har za a shekara 16 abin da aka yi maka bai fi ka ki ga ba me kake ganin a shekara uku ko hudu za ka iya kawo canjin da ba a kawo ba, don haka u dai ba mu so kasar ta koma yadda take a baya, don haka ne na ke bada tallafina ta wayar da kan mutane don haka sai na kirkiri wannan abin na sa masa suna Dankasa nake yin bidiyo na minti biyu nake dora shi a sohiyal mediya wanda kuma a yanzu na san babu inda ba a san da wannan ba saboda irin tsari da shi Dankasar ya zo da shi ne muna gaskiya.

To ko mene ne sakonka na karshe?
Sakona na karshe ga mutane shi ne ya zama an yi siyasa ta hankali wadda take an yi ta cikin wayewa domin da wanda kake so da wanda nake so za su yi ne su sauka kuma kuna nan a tare sana’arku da aikinku tare kuma duka abin da mutum zai yi ya tsaya ya yi domin Allah.

To madalla na gode.
Ni ma na gode.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!