Connect with us

LABARAI

Mutumin Da Aka Kora Saboda Faduwar Tazarcen Obasanjo Ya Rasa Kudin Magani

Published

on

Alhassan Haruna Malu, tsohon ma’aiakaci ne a ofishin yin katin shaidar zama dan kasa (DNCR) ya rasa kudin maganin jinyar da ke damun sa, wacce ta hana shi tafiya da kafafu kuma kurumta ma sa kunnuwa, sannan ta makanta idanunsa.
Alhassan Malu, wanda a yanzu ya na iya dan gani kuma ba ya ji sai da na’ura ya shaida wa wakilin LEADERSHIP A YAU LAHADI cewa, haushin rashin samun tazarcen Obasanjo a karo na uku ne ya sa a ka sallame shi daga aiki a shekara ta 2006, duk da cewa a lokacin ya na fama da jinya.
Alhassan Malu, wanda magidanci ne dan asalin jihar Gombe wakilinmu ya samu damar magana da shi ne ta hanyar rubutu, yayin da shi kuma ya bude baki ya yi magan gwari-gwari da kyar. A yanzu haka dai ya na da ‘ya’ya uku, amma sun rabu da matarsa, inda mahaifiyarsa ce ta ke kula da shi da ’ya’yan nasa duka.

Ya ce, tun da ya ke jinya sau daya karamar hukumarsu ta Yamaltu Deba ta tura shi jinya a cibiyar gwamnatin tarayya da ke Gombe ya yi wata biyu ta dalilin tsohon kansilansu, Alhaji Akwaye, inda bayan wata biyu a ka ce ya je ya cigaba da yiwa kansa jinya.
“Da kudin sallamana na aiki ya fito sai na ce a kai ni asibitin kashi na Dala da ke Kano. Su ka dauki hotona su ka ce kashina ne ya tsage, jijiyoyi su ka danne shi, shi ya sa ba na iya tafiya,” in ji shi.
Alhassan Haruna Malu ya kara da cewa, bayan da a ka yi ma sa wannan gwaji, sai a ka sake tura shi asibitin Malam Aminu Kano don su gane me ya sa ba ya jin magana da kunnensa, “inda su ka ce jijiyoyi ne su ka hadu, sun ce min zan ji magana, amma da na’ura,” in ji shi.
A cewarsa, bayan an gano matsalar a lokacin kuma kudinsa sun kare, sai ya koma asibitin Dala su ka dora shi a kan ya dinga zuwa gashin kashi.
Ya kuma ce gashin kashin da ya ke yi ya ba shi dama ya fara tsayawa, amma ya na kan zuwa gashin kashin ne a Kano sai ya nemi a dawo da shi cibiyar gwamnatin tarayya da ke Gombe, inda nan ma daga garin Kwadom ya ke fita zuwa zan ya na kashe Naira 1,200 kullum.
Alhassan ya kara da cewa, ya na wannan jinyar ne kuma sai yanar ido ta fito ma sa a ido, ya daina gani, inda ta kai ba ya ji ba ya gani kuma ba ya iya tafiya.
A na wannan yanayi ya ce, ya raba gonarsa ya sayar da rabi ya yi jinya har ganinsa ya dawo, amma bai jin magana kuma ba ya tafiya har yanzu.
Ya yi amfani da wannan damar ya yi kira ga gwamnati da ’yan siyasa da su taimaka ma sa ya samu ya yi jinya tunda ya na sa tsammanin zai warke.
Daga nan sai ya ce, ya taba neman taimako a wajen tsohon dan majalisar su na tarayya, hon. Shu’aibu Galadima, amma bai samu ba ya je wajen Habu Mu’azu don ya hada shi da Sanata Danjuma Goje, sanatan da ke wakiltar su daga Gombe ta Tsakiya ba, ballantana su hadu ba.
Komai a dakinsa ya ke yi, bai iya taka wa balle ya je bandaki, inda daga cikin daki sai dai ya yi rarrafe ya fito baranda kuma kafafunsa sun kumbura, kashi kuma ya fito ma sa a gwiwar kafarsa. Hakan ta sa ya ke neman taimakon, don ya koma asibitin kashi.
Don haka sai ya ce, ga mai niyyar taimaka ma sa za a iya kiran dan uwansa mai suna Nasiru ta wannan lambar 08088806824.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!