Connect with us

WASANNI

Shin Ko Ka San Cewa Har Yanzu Solkjaer Bai Yi Abin Kirki A Man U. Ba?

Published

on

Tabbas na san wasu za su yi mamakin a ce har yanzu kociyan Manchester United na rikon kwarya, Ole Gunnar Solkjaer, bai yi abin kirki a kungiyar ba. Wannan ya biyo bayan cewa, akwai abubuwa da dama da ya kamata a duba kafin a ce ya fi Mourinho nuna bajinta.
Tun bayan da kungiyar ta tabbatar da shi a matsayin kociyan kungiyar, Solkjaer ya jagoranci kungiyar wasanni biyar kuma duk ya samu nasara da gagarumin rinjaye kuma da irin sakamakon da magoya bayan kungiyar su ka dade ba su gani ba.
Kawo yanzu kungiyar ta buga wasanni biyar a jere a hannunsa kuma duk ta na samun nasara, inda ta samu nasara da ci 5-1 a kan kungiyar kwallon kafa ta Cardiff City yayin da kuma rabon da kungiyar ta samu nasara da kwallaye biyar tun lokacin tsohon kociyan kungiyar, Sir Aled Ferguson a wasansa na karshe a kungiyar da su ka buga 5-5 da kungiyar Westbrom Albiom a shekara ta 2013.
Bayan samun nasara a kan kungiyar Cardiff, Manchester United ta samu nasara a kan kungiyar Huddersfield da Bournemouth da kungiyar Newcastle United, sai kuma nasarar da su ka samu a kan kungiyar Reading a gasar cin kofin kalubale, wato FA, ta kasar Ingila.
To, sai dai kenan hakan ya na nufin cewa, tuni Mourinho ya gama wakiltar kungiyar a manyan wasannin gasar na zagayen farko kuma masana su na cewa Mourinho ma zai iya samun nasara a wadannan wasannin da Solkjaer ya samu nasara yayin da wasu su ke ganin akwai wasan da ba zai iya samun nasara ba, sannan kuma ba zai samu damar zura kwallaye da yawa ba kamar yadda Solkjaer ya yi a yanzu ba.
Kawo yanzu dai tun farkon fara aikin koyar da kungiyar Manchester United Solkjaer ya samu nasarar wasanni biyar kuma a cikin wasannin da ya samu nasara ya zura kwallaye 16 sannan kuma an zura ma sa kwallaye uku.
Za a iya cewa, an samu canji duba da yadda kungiyar ba ta iya zura kwallaye sama da uku a raga a lokacin Jose Mourinho, sannan kuma a na yawan zura ma ta kwallo a raga, wanda hakan ya sa yanzu a ka zura ma ta kwallaye kusan 32 a ragarta.
Sai dai duk da haka shi ma Solkjaer ya yi kokari sosai duba da yadda ‘yan wasan kungiyar yanzu su ke buga wasa yadda yakamata ba kamar lokacin Mourinho ba sannan wasu daga cikin ‘yan wasan kungiyar kokarinsu ya karu sosai.
Canjin Da A Ka Samu A Kan Pogba Da Rashford Da Martial
Wasa na karshe da Mourinho ya jagoranci kungiyar kwallon kafa ta Manchester United shi ne wasan da kungiyar ta sha kashi a hannun kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da ci 3-1 kuma a wasan Mourinho bai yi amfani da dan wasa Pogba ba.
Da man dai akwai rikici mai karfi tsakanin dan wasan da shi kansa Mourinho wanda a kwanakin baya sai da a ka fitar da wani fefen bidiyo inda a ka nuna mutanen biyu su na mayarwa da juna Magana a filin daukar horon kungiyar.
Wasu na ganin daya daga cikin dalilan da ya sa kungiyar ta sallami Mourinho bai wuce rashin jituwa da wasu daga cikin ‘yan wasan kungiyar ba da su ka hada da shi kansa Paul Pogba wanda ya fi kowanne dan wasa tsada a kungiyar.
Sai dai tun bayan tafiyar Mourinho Solkjaer ya cigaba da amfani da Pogba a wasannin kungiyar kuma kawo yanzu Pogba ya ci kwallaye hudu a raga sannan ya taimaka an zura kwallaye uku har ila yau dan wasan ya samu kyautar dan wasan da ya fi kowanne dan wasa kokari a watan Disambar da ya gabata wanda kungiyar ta ke bayarwa.
Shi ma dan wasa Marcus Rashford, wanda ba ya kokari a lokacin mai koyarwa Jose Mourinho, yanzu tauraruwarsa ta na haskawa kuma ya zura kwallaye uku cikin wasannin da ya buga wa kungiyar a karkashin mai koyarwa Ole Gunnar Solkjaer.Har ila yau yanayin yadda dan wasan ya ke buga wasa cikin farin ciki da kuma yadda ya ke gudu a fili ya canja ba kamar a lokacin Mourinho ba sannan kuma ya na taimaka wa kungiyar ta na zura kwallo a raga.
Anthony Martial dan wasa ne wanda ba sa jituwa da Mourinho, wanda kusan za a iya cewa tunda Mourinho ya je kungiyar su ka fara takun-saka tsakaninsa da Martial, sai dai shi ma tun bayan tafiyar Mourinho yanayinsa ya canja a kungiyar.
A farkon wanann kakar Martial, ta bakin wakilinsa, ya bayyana cewa ya na son barin kungiyar kwallon kafa ta Manchester United domin ba ya samun damar buga wasa a kowanne lokaci kuma haka kawai ba saboda dalilin jin ciwo ba.
Kusan za mu iya cewa da Pogba da Rashford da kuma Martial kwallonsu ta canja a kungiyar sannan kuma banda su akwai ‘yan wasa irinsu Lingard da Mata wadanda su ma tafiyar Mourinho ta sa su na buga kwallo mai kyau.
A takaice dai a na ganin rashin kokarin da kungiyar ta rika yi a baya, ba gazawar Mourinho ba ce, illa dai zagon kasa da wasu ke zargin wasu ’yan wasa da aikatawa, don kawar da kociyan da ba su kauna daga kulab din.
Ziyarar Da Sir Furguson Ya Kai Filin Daukar Horon Kungiyar
A kwanakin baya tsohon kociyan kungiyar, Sir Aled Ferguson ya kai ziyara filin daukar horon kungiyar da ke Carrington a birnin Manchester, inda kuma ya tattauna da ‘yan wasan kungiyar da masu koyar da su, za a iya cewa ta taimaka.
Sai dai tun kafin ziyarar tasa Solkjaer ya bayyana cewa zai yi kokarin ganin ya dawo da salon yadda kungiyar ta ke buga wasa tun lokacin mai koyarwa Sir Ferguson ta hanyar yawan kai hare-hare kamar yadda a ka san kungiyar da kuma yawan zura kwallaye a raga ba kamar yadda Mourinho ya koyawa kungiyar salon kare gida ba.
Cikin wasanni biyar kungiyar ta zura kwallaye 16 wanda wannan sabon abu ne a kungiyar duba da yadda kungiyar tayi masu koyarwa tun daga kan Dabid Moyes da Ryan Giggs (rikon kwaryar wasanni uku) sa Luis Ban Gaal da kuma Jose Mourinho wadanda ba sa zura kwallaye a raga koda a ce sun samu nasara a wasa.
Aikin Da Ya Ke Gaban Solkjaer
Kamar yadda ya ke tun farko wasanni biyar din da Solkjaer ya jagoranci kungiyar wasanni ne wadanda duka da kananan kungiyoyi ya buga domin acikin kungiyoyin Cardiff da Huddersfield Town da Bournemouth da Newcastle duk babu kungiyar da take cikin kungiyoyin da suke goman farko na gasar firimiya, haka ma kungiyar Reading wadda United din ta buga gasar cin kofin kalubale na FA su basa buga gasar firimiya ma gaba daya.
A yau Manchester United zata buga babban wasa da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, kungiyar da taje a har filin wasa na Old Trafford ta doke Manchester United daci 3-0 acikin watan Agustan shekarar data gabata.
Wannan wasa shine wasan da zai tabbatar da cewa Solkjaer yayi kokari ko kuma baiyi ba ko kuma zai nuna cewa shin yakamata kungiyar ta mayar da kwantaragin Solkjaer na din-din-din kamar yadda wasu daga cikin tsofaffin ‘yan wasn kungiyar da ‘yan jaridu da magoya baya sukeso.
Tottenham dai itace a matsayi na uku akan teburin gasar firimiya yayinda wadda take mataki na daya wato Liverpool ta basu tazarar maki shida yayinda Manchester City kuma wadda take mataki na biyu ta basu maki biyu.
Ga Wasu Daga Cikin Wasannin Da Su Ke Jiran Solkjaer
Tottenham vs Manchester United 13/01/2019
Arsenal vs Manchester United (FA CUP) 26/01/2019
Manchester United vs PSG 12/02/2019
Manchester United vs Liverpool 24/02/2019
PSG vs Manchester United 06/03/2019
Arsenal vs Manchester United 09/03/2019
Manchester United vs Manchester City 16/03/2019
Hakan yana nufin bayan buga wasa da Tottenham da kuma wasa da Arsenal a gasar cin kofin FA Cup a karshen wannan watan, daga watan biyu zuwa watan uku Manchester United zata buga wasanni masu zafi da suka hada da wasanni guda biyu da kungiyar PSG gasar cin kofin zakarun turai da kuma wasannin firimiya da kungiyoyin Arsenal da Liverpool da kuma Manchester City.
Idan har Solkjaer yayi kokarin samun kashi 75 cikin 100 na wadannan wasannin tabbas za’ace yafara dawo da kungiyar hayyacinta kuma ita kanta kungiyar zatayi nazarin tabbatar dashi a matsayin mai koyarwa mai cikakken iko.
Magoya bayan Manchester United dai tuni suka fara murnar ganin salon da aka san kungiyar na buga wasa yafara dawowa kuma samun nasarar wasannin da suke gaban kungiyar shine zai tabbar da kungiyar tafara dawowa hayyacinta.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!