Connect with us

LABARAI

Wani Mutum Ya Kashe Kansa A Legas

Published

on

Wani mutumin da ba a tantance sunansa ba, mai matsakaicin shekaru, a safiyar jiya Asabar ne ya rataye kansa da kansa a jikin bishiya da ke layin hanyar Catholic Mission Road kusa da kotun daukaka kara da ke Legas.
Mutumin mai da ya rataye kansa ya na da launin mutunen Ankara, an iske shi ya na rataye a jikin bishiya wanda ya rataye kansa da igiya mai kauri.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN, ya labarto cewar jama’a sun yi ta jimamin yadda lamarin ya faru, inda jama’an suka yi cinciridun a wajen da mutumin ya rataye kansa suna kallon abun mamaki yadda ya rataye kansa, inda wasu ke mamakin mene ne kuma dalilinsa na daukan wannan matakin.
Dan sandan da a ka riska a wajen da abun ya faru, ya tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai ya ce ba zai tabbatar da cewar ga hakikanin abun da ya faru ko bayyana takamaimai abu guda kan wannan lamarin ba har sai sun kammala gudanar da bincike na sosai kan lamarin.
Ya ce, sun yi iyaka kokarinsu wajen duba gabar da yamma ko za su ga wani abu, kana sun kuma caje dukkanin aljihunan mamacin domin ko Allah zai sanya su ga wani abun da zai iya alamtashi amma har zuwan lokacin da likita zai tabbatar da musu da mutuwarsa basu gano shi din waye ba.
Wasu daga cikin mutanen da suka kasance cikin jimami a wajen da abun ya faru, suna masu daukan hotuna da nuna kaitonsu, saidai dukkaninsu babu wani da ya iya gano wanda ya rataye kan nasa a jikin bishiyar.
Mista Ige Adedoja, wani mazaunin yankin ne, ya shaida cewar tun lokacin da mutane suka gano shi a rataye babu wanda ya taba jikinsa har sai da likita ya zo ya tabbatar da mutuwarsa.
Ya ce, mutumin ya kasance a rataye ne kamar yadda suma suka ganshi a jikin bishiya sai bayan da likitan ya zo ya fayyace komai.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!