Connect with us

LABARAI

Zaben 2019: Jam’iyyun Adawa Sun Yi Bore Kan Barin Amina Zakari Matsayinta

Published

on

*Sun Jero Wasu Bukatunsu

Sama da jam’iyyun adawa 50 cikin har da babban jam’iyyar adawa PDP a karkashin lemar hadakar jam’iyyu ta ‘Coalition of United Political Parties’ (CUPP), sun ki amincewa da sharudda sama da guda takwas na zaben 2019 da hukumar zabe ta fitar da su a matsayin ka’idar gudanar da zabe.
Har-ila-yau, jam’iyyun sun nemi a sauya Amina Zakari daga shugabar da ke sanya ido kan tattara sakamakon zaben kasar, a bisa shakkun da su ka nuna kan yin adalci ko sahihancin sakamakon da za ta tabbatar.
A cikin wata kwafin sanarwar da hadakar jam’iyyun adawar CUPP suka fitar a jiya, ta hanun jami’in hulda da jama’a na jam’iyyun, Cif Ikenga Ugochinyere, ya ce, wadannan sabbbin tsarin za su kawo illa a cikin rumfunan zaben 2019.
Cif Ugochinyere ya shaida cewar jam’iyyun sun kuma ki amincewa da tsarin da zai baiwa masu zabe damar yin zabe da katin zabe na dindindin amma kuma sunayensu baya cikin jerin rijistan wadanda suka yi rijistan yin zabe.
Jam’iyyun sun kuma nuna rashin kwarin guiwarsu akan shugaban INEC na kasa Prof. Mahmood Yakubu, a bisa matakan da suke cewa ya dauka a daidai wannan lokacin na fitar da waje jerin sharuddan kada kuri’u.
Wakazalika, jam’iyyun sun kuma gabatar da wasu jerun bukatun da suke son INEC ta sauya ko ta yi musu domin samun aminci kan sashihancin zaben a cikin ransu, da suka hada da cewa, “Jam’iyyun nan suna bukatar a yi dubiya kan zaben 2011 da na 2015 domin hakan zai bayar da dama a toshe dukkanin wata shirin yin magudi a zaben 2019 da ke tafe, domin samun nasarar zabe mai nagarta.
“Jam’iyyun siyasa suna kuma bukatar a sanar da adadin masu yin zabe a lokacin da ya kamata, kuma a taskace adadin a baiwa wakilan jam’iyyu su gabanin fara kada kuri’u a wajen zabe, yin hakan zai taimaka wajen ganin adadin kuri’u da zai fito daga kowace wajen zabe,” Inji Sanarwar
“Jam’iyyun nan suna bukatar a tsaida amsar katin zabe na dindindin kwanaki 10 gabanin fara gudanar da zabe, don hakan zai bayar da damar a tantance adadin mutanen da suka amshi katinan zabensu,” A cewar sanarwar.
Sannan kuma jam’iyyun sun nemi a yi hadaka da jami’an sanya ido da wakilan jam’iyyu wajen tabbatar da gudanar da sahihin zabe.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, “Sannan kuma jam’iyyun nan sun ki amincewa da kirkirar ko kuma yin amfani da wani rumfar zabe a asirrince, sannan, muna kuma muna son a fitar da dukkanin adadin rumfunan zabe,” Inji kungiyar hadakar jam’iyyun siyasa.
CUPP, ta kuma ce, “Jam’iyyun siyasa sun nemi a sauya Amina Zakari daga kasancewa babbar jam’iyar tattara sakamakon zabe, a maye gurbinta da kwamishina da ke kula da aiyuka, Prof. Okechukwu Ibeanu domin tabbatar da gudanar da sahihi kuma tsaftaccen zabe ba tare da wani son kai ko wariya ba,” Inji Sanarwar ta jam’iyyun adawar ‘Coalition of United Political Parties’ (CUPP).
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!