Connect with us

LABARAI

An Bukaci ‘Yan Siyasa Da Su Guji Kalaman Batanci

Published

on

Anyi kira ga al’ummar kasar nan da cewa zabe da yake tinkarowa su kula su zabi cancanta duk wanda suka ga yana da kishi da zai kawo ci gaba da gyara matsalolin kasar nan su bashi kuri’arsu.Wani dan kasuwa kuma dan siyasa a jihar Kano. Alhaji Nasiru Husaini Agalawa ya yi wannan kiran da yake zantawa da manema labarai bayan karramashi da kungiyar dalibai ta kwalejin nazarin ilimin addini da shari’a ta Malam Aminu Kano ta yi.
Ya ce, wannan zabe da yake tahowa a ci gaba da addu’a ta samun shugaba nagari da zai ceto kasar nan daga halin da take yi addu’a a bai wa Allah zabi. Sanna su kuma yan jarida su rika wayar wa da mutane kai a kan su san siyasa bata a mutu ko ayi rai bace kowa yayi ra’ayinsa. Duk duniya yan jarida su suke sa abubuwa a tsari, su ci gaba da wayar da kai na yanda ya kamata ayi siyasa.
Alhaji Nasir Husain Agalawa Kafin Agur ya bayyana gamsuwarsa da yanda wasu yan’jam’iyya a jihar Kano suke gudanar da yakin neman zabensu a jihar Kano cikin tsari da lumana ba tare da wata hayaniya ba, ba yawo da makamai ko kuma sanya matasa a yanayi da bai dace ba, wanda hakan abune mai kyau da ya kamata ace haka dukkan yan siyasa suke.
Sannan kuma ya koka da yanda wasu yan siyasar suke yawon neman zabe da makamai da hakan ke jawo anata asara rayukar da cea hakan bai dace ba. Sannan kuma suna ganun hoton wasu yan takara suna yaga wa wannan ba daidai bane.Bai kamata ace kano da take da musulmi kashe 99 ace ana yakin neman zabe ana rasa rayuka ba.
Alhaji Nasiru Agalawa Kafin Agur yace yan siyasa kamata ya yi kowa yaje ya tallata manufarsa ya fadawa mutane abin da yake ganin zai yi na kawowa al’umma ci gaba amma ba a rika neman mulki ko a mutu ko ayi rai ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!