Connect with us

RAHOTANNI

An Gudanar Da Maulidin Annabi (SAW) Na Kasashen Afirka Karon Farko A Kebbi

Published

on

Hadaddar Kungiyar Darikar Tijjaniya ta kasa ta gudanar da bukin maulidin Nabi (S.A.W) na kasashen Afirka a kasar Nijeriya karon na farko a babban Birnin, jihar ta kebbi . Inda mabiya darikar Tijjaniya na duk fadin kasar Nijeriya da kasashen Afirka da kuma sauran wasu kasashen duniya sunyi tattaki don haduwa a jihar kebbi domin gudanar da maulidin na tunawa da ranar haihuwa manzon Allah Muhammadu Rasulula ( S.A.W) da kuma gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya, tsaro ga ‘yan Nijeriya da kasashen duniya baki daya.
Taron bukin maulidin na kasa da kasa an gudanar da shi ne a filin gudanar da taro na Haliru Abdu dake a cikin garin Birnin-kebbi da kuma dakin taron na masaukin shugaban kasa da ke a Birnin-kebbi a jiya wanda an kwashe kwanaki uku ana gudanar da bukin maulidi na kasa da kasa a Birnin-kebbi.
Yayin gudunar da bukin maulidin a Birnin-kebbi, mambobin kungiyar ta Tijjaniya da suka hadu a wurin taron bukin sun gudanar da saukar al-kur’ani har sau 313 domin neman Allah ya sa albarka da kuma samun zaman lafiya a kasarmu Nijeriya da kuma gudanar da zaben 2019 a cikin kwanciyar hankali batare da wata matsala.
Har wa yau shugabannin darikar Tijjaniya a cikin tsarin gudanar da bukin maulidi sun kai ziyara a gidan Yari, asibiti da kuma sauran wasu wurare don gudanar da wa’azi da addu’o’i na samun zaman lafiya da kuma tsaro ga kasa da kuma dukiyar ‘yan kasa.
Tattakin ziyarar ya samu jagorancin sheikh Mahi Ibrahim Nyass wanda ya wakilci Sheikh Ahmad Tijjani Ibrahim Nyass inda ya karanta wasu ayoyin al-kur’ani da kuma gudanar da addu’a ga kasar Nijeriya da kuma zaman lafiya a kuma gudanar da zaben 2019 a cikin tsanaki.
Hakazalika manyan malamai, shehunnai da kuma sauransu sun gabatar da kasidu a wurin bukin maulud a Birnin-kebbi inda farfesa Jidda Hassan na kasar Senegal da babban sakataren Jama’atu Ansarul Tijjaniya Sayyadi Alkasim Yahaya sun kayi kira ga ‘yan uwa musulmi dasu rika nuna soyaya su ga Allah da kuma mason manzon Allah Muhammadu Rasulalla (S.A.W) a koda yaushe sun kuma girmama sunan Allah ta hanya gudanar da maulidi don tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah Muhammadu Rasulalla( S.A.W).
Shi ma Sheikh Ali daga kasar Senegal ya roki Allah da ya kawarda aikin ta’addancin a kasar Nijeriya da kuma shawartar ‘yan kasar dasu baiwa shugaba Muhammadu Buhari goyon baya domin iya magance wasu matsaloli dake damuwar kasar a halin yanzu.
A nasa jawabi a wurin taron shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari wanda ministan shari’a na kasa ya wakilta a wurin taron bukin maulud a jihar ta kebbi , Barrister Abubakar Chika Malami ya bayyana wa jama’ar kasashen duniyar cewa; “tsaron da aka samu a kasar Nijeriya kwazo ne irin na shugaba Muhammadu Buhari yayi kan tabbatar da ya samar da tsaro ga ‘yan kasa da kuma kariya ga dukiyoyinsu da kuma samar da cigaba mai amfani ga jindadi da walwala ga jama’ar da ake mulki a kasar Nijeriya.”
Haka kuma yayi amfani da wannan dama don kira ga ‘yan kasar Nijeriya dasu taimaka wa gwamnatin wurin ganin cewa an zauna lafiya a jahohin kasar nan musamman zaben 2019 na karatowa da fatar cewa zasu gudanar da zaben ba tare da samun wani tashin hankali ba. Yace daya daga cikin amfanin samar da tsaro shi ne gashi ana gudanar da bukin maulidi na kasa da kasa a cikin jihar kebbi kimanin kwanaki uku wanda duk inda kaduba zakagan jami’an tsaro ko’ina saboda daya a tabbatar da cewa an gudanar da wannan gagarumin taron lafiya kuma kowa ya koma gidansa lafiya batare da wata matsala ba.
Sannan kuma ya tabbatar wa shugabannin darikar Tijjaniya cewa; ”gwamnatin Muhammadu Buhari a shirye ta ke ta bada duk irin gudunmuwar da ta dace don ganin cewa darikar Tijjaniya ta cigaba da wayar da kai ‘yan kasa kan zaman lafiya da kuma cigaba wa kasar Nijeriya addu’a “. Bugu da kari ya nuna jindadinsa kan samun irin wadannan shugabannin darikar Tijjaniya na tunanin gudanar da addu’o’i da kuma saukar al-kur’ani don neman samun daurewa zaman lafiya a kasar Nijeriya saboda haka gwamnatin tarayya na godiya ga irin karramcin da kuma goyon bayan da ake bata”.
Daga karshen ya roki shugabannin darikar Tijjaniya na kasa da kuma na sauran jahohin kasar nan da zaben 2019 a kara karatowa saboda haka yake neman alfarma na a ranar zabe idon Allah yakai mu dasu fito kwaida kwarkwata su zabi Muhammad Buhari a matsayin shugaban kasar Nijeriya karo na biyu da kuma sauran ‘yan takara na jam’iyyar APC a duk fadin kasar nan.
Da yake jawabinsa tun farko Gwamnan jihar kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana jin dadinsa kan zabar jiharsa a matsayin jihar da za a gudanar da maulidi na kasashen Afirka karo na farko a kasar Nijeriya a jihar kebbi. Gwamna ya cigaba da cewa “ wannan taron maulud na kasashen Afirka da ake gudunar wa a kasa Nijeriya kuma jihar kebbi karo na farko a jihar da kuma kasar shiya nuna cewa Allah ya Albarkaci Nijeriya da shugaba mai son jama’asa da kuma basu cikaken goyon baya ga harkokinsu a duk kasar da suka fito ko kuma addinin da suke.
Ya kuma yaba wa shugabannin da kuma mambobbin darikar Tijjaniya kan gudanar da addu’o’i ga kasa da kuma ‘yan kasa don samun zaman lafiya da kuma samun tsaro da kwanciyar hankali a kasa bakin daya. Daga karshe yace” gwamnatin jihar kebbi a shirye take da duk lokacin da irin wannan taron bukin ya tashi ta bada nata gudunmuwa da kuma goyon bayanta na ganin cewa an gudanar da irin wannan bukin mai albarka a jahohin kasa da kuma kasar baki daya. Ya kuma yiwa jama’ar da suka halarci taron maulud fatar komawa gidajensu da kuma kasashensu lafiya.
Wakilin LEADERSHIP A Yau daga Birnin-kebbi ya ziyararci wurin taron gudanar da maulidin inda ya ruwaito muna cewa an gudanar da maulidin Nabi don tunawa da ranar haihuwar manzon Allah Muhammadu Rasulalla (S.A.W) wanda aka hada mutane daga kasashen Afirka da kuma na duniya baki daya kama tun daga kasar Nijeriya, Nijar, Jamhuriyar Benin, Mali, Senegal, Cota, Ghana da kuma Togo, Moroko da sauransu duk sun halarci taron.
Haka kuma dukkan wadannan kasashe da suka halarci taron sun zo da manyan shehunansu da kuma magoya bayansu. Inda gwamnatin jihar kebbi ta dauki nauyin gudanar da maulidin Nabi (S.A.W) kama tun daga masauki har abinci da kudade don tabbatar da cewa an gudanar da taron maulidi Nabi a cewa nasara batare da wata matsalaba.
An samar da tsaro mai inganci inda har aka kammala taron bukin ba a samu wani rahoton tashin hankali ko wata hatsaniya ba. Hakazalika masu sayar da kaya da abinci sai godiya suke yi ga Allah kan irin cinikin da suka yi wurin taron bukin gudanar da maulidin Nabi da aka gudunar a jihar kebbi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: