Connect with us

RAHOTANNI

An Tattauna Bukatar Gwamnatin Tarayya Ta Kare ’Yancin Bil’adama

Published

on

A ranar Alhamis 10 ga watan Janairun 2019, Kungiyar Sulhuntawa da kare Hakkin Bil’adama wacce aka fi sani da ICRP a turance, ta gudanar da wani taro da ya shafi kare hakkin Bil’adama a birnin Tarayya Abuja. Taron ya gudana ne a dakin taro na Otel din Sabannah Suites dake Area 3 a Abuja. Inda Malaman Jami’a da Kungiyoyin Kare Hakkin Bil’adama da Dalibai da sauran su suka halarci taron. Daga cikin manyan baki da suka halarci taron sun hada da; Farfesa Dahiru Yahaya daga BUK da Farfesa Abdullahi Danladi daga ABU da Ndi Kato mai rajin kare hakkin Bil’adama da Kwamared Musa da dai sauran su.

Kungiyar ta bayyana Kanal Sambo Dasuki da Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa Zeenatuddeen Ibrahim da Kwamared Deji Adeyanju a matsayin wadanda gwamnati ke ci gaba da rike su ba bisa ka’ida ba duk da kuwa akwai umurnin kotu na cewa a sake su.
Shugaban Kungiyar, Kwamared Shu’aib Isa Ahmed, ya bayyana cewa; “Manufar wannan taron shi ne, domin mu zo mu hada kawukanmu a matsayinmu na ‘yan Nijeriya tare da kuma tattaunawa makomar kasarmu.” Ya ci gaba da cewa, “Yanzu komai ya tabarbare a Nijeriya, wanda ya hada da bangaren tattalin arziki da tsaro da take hakkin bil’adama da kuma rashin bin doka da oda daga hukumomi da sauran su.” Inji shi.

Sai dai ya tabbatar da cewa, ya kamata a ce ‘yan Nijeriya sun fahimci cewa muna da bambanci a tsakaninmu, amma dole ne mu zauna tare. Ya nuna takaicinsa na yadda a da bamu rigingimu a tsakanin Musulmi da Kirista a kasar nan a shekarun baya, “Amma yanzu mene ne yasa ake samun wadannan rigingimu? Rashin girmama fahimtar juna. Manufarmu shi ne tabbatar da Nijeriyar da kowa zai yi alfahari da ita. So muke mu hada kan al’umma, mu rika tunatar da al’umma muhimmancin zaman lafiya, sannan mu rika goyon bayan wadanda ake zalunta ba tare da la’akari da addininka ko kabilarka.” Inji Kwamared Shu’aib.
Da yake nasa jawabinsa, babban mai jawabi a wurin taron, Farfesa Dahiru Yahaya ya bayyana cewa, babbar matsalar da ake fuskanta a kasarnan shi ne, “Kasar ta fara zama kamar babu shugabanci.” Ya ce, domin yanzu an koma sam hukumomi basa bin doka da oda. Ya kara da cewa, babban abin takaicin shi ne, kowa ya san da wannan, amma kowa bai damu ba, hakazalika ma shuwagabannin ma suna nuna halin ko in kula.

Da yake magana dangane da tabarbarewar tsaron a kasar nan, ya ce, matsalar rashin tsaro ya faro daga Maiduguri tun zamanin tsohon shugaban kasa Marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua, ya ce yanzu abin ya dawo arewa maso yamma na kasar nan.
Ya nusasshe da yadda cewa, jami’an Soji ya kamata su zama ayyukansu na kare kasa ne, ba na cutar da al’umma ba. Ya kara da cewa, hakazalika ya kamata jami’an tsaron ‘yan Sanda su zama abokan ‘yan kasa ne. Ya nuna muhimmanci gwamnati ta rika sauraren al’umma, domin a cewarsa, karfi ba ya maganin komai. Ya shawarci shuwagabannin kasarnan da su zama suna fahimtar al’amura kafin su rika daukar matakai a kan su. Ya lurantar da mahalarta taron yadda tabarbarewar tsaro yake da da karuwa a kasar nan. Ya ce, “Da a arewa maso gabas ne, yanzu yana aukuwa a arewa maso yamma.” Ya nuna yadda kafin ‘yancin kan kasar nan da bayan ‘yancin kai, yadda kasar ake zaune lafiya a tsakanin mabiya addinai. Ya ce; shi yana ganin abubuwan da suka haifar da matsaloli a tsakanin addinai, shi ne yadda aka rika kawo fahimtoci daban-daban daga wajen kasar nan.

A hirarsa da manema Labarai ciki har da Leadership A Yau, Farfesa Dahiru Yahaya ya tabbatar da cewa, manufar jawabinsa a wurin taron shi ne, ana da bukatar hadin kan al’umma domin magance matsalolin da suke fuskantar kasar nan wanda ya hada da, cin hanci da rashawa, kabilanci da rashin bin doka da oda na kasa, rashin bin umurnin kotu. “Muna da bukatar dukkanninmu mu hada kawukanmu ba tare da bambancin yanki ko fahimta ba.” Inji shi.
Farfesa Dahiru Yahaya, ya jaddada cewa; yanzu babu wadansu Shuwagabannin Musulmi wadanda suke kare hakkin Musulmi a kasar nan.
Har wala yau a wani bangare na hirarsa da manema labaran, Farfesa ya ce; tabbas kasar nan ana da bukatar hadin kai, ana da bukatar daina nuna kabilanci da ta’assubanci, ya ce, kuma dole ‘yan Nijeriya su cire tsoro domin cimma nasara. Ya ce, “Arewa na matukar fama da matsaloli. Boko Haram ya fara a arewa maso gabas. Yanzu kuma ga wata Boko Haram ta bulla a Zamfara da Sakkwato.”

A nasa jawabin a wurin taron, Farfesa Abdullahi Danladi, Malami a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, ya bayyana cewa; ko ma a ya ya muke, dukkanninmu dai mu samu kanmu ne a wata kasa da ake cewa Nijeriya. Inda ya ce, zaka samu kowa da addinin da yake yi. Da yake karin bayani, Farfesan ya ce, “Shin to ta ya ya zamu rayu a wannan kasar? Kana da bukatar sai kowa ya zama Musulmi? Ko kuwa dole sai kowanne Kirista ya yi kokarin maishe da kowa Kirista? Wannan a aikace ba mai yiwuwa bane.” Inji shi.
Har wala yau ya ci gaba da cewa, Manzon Allah (S) abin koyi ne ga Musulmi. Inda ya ce, da Manzon Allah ya yi hijira daga Makkah zuwa Madina, Manzon Allah ya samar da doka wacce Musulmi da Kirista da Yahudu suka zauna tare. Ya ce, addinin Musulunci, addinin zaman lafiya ne. Domin a Madina, kowa ya zauna lafiya da Musulmi. Ya ce; a don haka ya kamata Musulmi su yi koyi da Manzon Allah ne, domin Musulunci bai koyar da takurawa da gallazawa wadanda ba Musulmi ba. Ya kara da cewa; “Musulunci yana kira ne zuwa ga ‘yanci. Idan har kai mutum ne, kana da damar rayuwa. Kuma kana da damar zabar addinin da kake son ka yi. Babu tilasci a addini.”

Ya ci gaba da cewa, idan har tilasta maka aka yi ka zama Musulmi, tabbas wannan ba Musulunci kake ba. Domin a cewar Farfesan, “Musulunci shi ne mika wuya ga Allah ta’ala bisa yarda da sakonsa.” Ya ce; a kasar nan akwai shuwagabannin da suke takewa mutane hakkinsu, marasa gaskiya da kishin al’umma. Ya ce, “Wacce irin gwamnati ce muke da ita wacce ake kashe ‘yan kasarta?” Ya ci gaba da cewa; “Mutanen da ake ci gaba da rikewa ba bisa ka’idar bin doka ba, idan har an san suna da laifi, gwamnati ta kai su kotu mana. Dasuki kotuna sun ba da belinsa, amma har yanzu gwamnati ta ki sakinsa. Shaikh Zakzaky ba belinsa aka bayar, shi ne ya kai su kotu a kan take masa hakki, kuma a karshe ya yi nasara. Kotu ta ce ba shi da wani laifi, a sake shi, amma har yanzu gwamnati ta ki bin umurnin kotu. Abin da ke gabanta shi ne kawai ta sake cin zabe.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!