Connect with us

LABARAI

Gwamnati Za Ta Yi Maganin Masu Son Kawo Rikici A Jihar Kogi –Gwamna Bello

Published

on

Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya yi alkawarin hukunta duk wanda aka samu da hannu a samarwa da matasa da makami da kuma tayar da hankalin jama’a a fadiun jihar.
Ya yi wannan alkawarin ne a jiya a garin Kano a yayin da yake jawabi ga shugabanin kungiyar ‘yan kabilar Ebira mazauna garin Kano ‘Ebira Peoples Association’ a taron liyafa da suka shirya masa a otal din ‘Bristol Palace Hotel’ Kano.
Ya kuma tabbatar da dalilin da gwamnatinsa take daukar lamarin tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar da matukar mahimmanci kuma ya yi alkawarin ba zai yi kasa a gwiwa ban a banin bayan makiya jihar, masu wannan halin za su fuskanciu fushin hukuma da zaran an kama su.
Gwamnan ya bayyana cewa, yana da masaniyar menene tsaro, a kan haka ne ya dauki lamarin tsaron da matukar mahimmanci a kan haka ne yake neman goyon bayan ‘yan kabilarsu don ya samu nasara samar da zaman lafiya yadda ya kamata a fadin jihar.
“Hakki ne na dukkanmu na kawo canji a cikin al’ummarmu. Ya da matukar mahimmanci kada mu dora wa wasu matsalolin da muke fuskanta mu kuma rika numa hali na gari da kuma yin kokarin zaman lafiya a dukkan lokacin “ inji shi.
Gwamnan ya kuma yaba wa ‘yan kabilar Ebira a bisa aiki tukuru da kuma runumar sana’a a duykkan inda suka samu kansu, ya kuma bukaci su ci gaba bayyana haliu na gari a dukk inda suka samu kansu musamman al’ummar da suka zaune das u a jihohin da suka sama kansu.
Ya kuma mika godiyarsa ga kungiyar a bisa goyon bayan da suke ba gwamnatinsa tun day a dare karagar mulkin jihar, ya kuma bukaci su ci gaba da bashi irin wannan goyon bayan a ci gaa da samun nasarar day a kamata.
Gwamna Bello ya kuma bayyana cewa, zaben shekarar 2019 na da matukar mahimmanci don a ci gaba da ayyukan aihairin da aka fara a saboda haka ya bukaci dukkan ‘yan kabilar Ebira das u ba jam’iyyar APC goyon baya don a samu nasarar da ya kamata a zaben dake tafe.
Ya kuma ce, zaben shugaba Muhammadu Buhari a zaben dake tafe yana da matukar mahimmanci don ci gaba Nijeriya da ‘yan Nijeriya, a kan haka ya nemi goyon bayan ‘yan kabilar Ebira na su ba gwamna Umar Ganduje na jihar Kano State da sauran ‘yan takarar jam’iyyar APC a zaben dake tafe na 2019.
Taron ya samu halartar sakin al’ummar kabilar Ebira ‘Ohinoyi of Ebira’ na jihar Kano dana jihar Jigawa, Alhaji Aliyu Abdulmalik da Mahmod Odidi Ozigi da kuma shugabar mata na kungiyar na jihar Kano, Hajia Maimunat Salihu da shugaban matasa, Adam Shuaibu das aura jama’a.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!