Connect with us

LABARAI

INEC Ta Sake Samar Da Katin Zabe 2,045 Da A Ka Sace A Akwa Ibom

Published

on

Shugaban hukumar zabe na jihar Akwa Ibom, Mista Mike Igini, ya bayyana cewa, a sake samar da katin zabe 2,045 da aka sace a karamar hukumar Okobo, wanda aka sace kwanakin baya.
Mista Igini, ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da manema labarai a garin Uyo ranar Lahadi, za a ba masu katin zaben na ainihi ya kuma tabbaar da cewa, babu wanda za a ware a zaben da za a fara gudanar wa rana 16 ga watan fabrairu 2019.
Bayani ya nuna cewa, an sace katuna zaben ne a wani tashin tashin hankalin day a aukua zaben fidda da gwani a da aka gudanar a shekarar 2018 a karamar hukumar Okobo ta jihar Akwa Ibom.
Ya kuma kara da cewa, za a fara raba katin kuri’un ne kafin a fara ragistar mazabun da za a fara ranar 16 ga watan Janairu a jihar.
“A garin Abuja muka samar da katimn zabe, wadanda suka sace katin kuma da tunanin mayar da jama’armu saniyar ware sun ji kunya, mun sake buga sabo kuma a wannna makin ne za a fara rabawa’’.
Igini ya kuma kara da cewa, katin zaben da aka sace suna waje na musamman ne da aka boye har na tsawon wata 2 amma a ka sace.
Ya kuma kara bayyana cewa, wasu daga cikin katin zaben ba za su kai ga masu shi ba saboda ko sun riga sun mutu ko kuma masu su sun bar zama a jihar ko kuma sun bar kasar gaba daya.
Daga nan kuma Igini ya yi zargin cewa, wasu ‘yan siyasa sun shigo da ‘yan kasashen waje inda suka yi ragista a yayin da ake gudanar da harkar rajista a jihar kwanakin baya.
“Akwai wasu muaten da aka shigo da su daga wasu jihohi makwabta inda suka yi ragsita, irin katin wadannan mutane ba za su samu karbuwa ba,” inji shi.
Ya kuma ce ya zuwa yanzu a kwai katin zabe fiye da 286, 928 da ba a karba, an kuma karbi katin zabe fiye da Miliyan 1.72 a fadin jihar.
“Mun samu matukar karuwar jama’ar da suka karbi katin zabe a wannan karo a jiharmu.
“ya zuwa yanzu fiye da katin zabe Miliyan 1.72 mutahne jihar Akwa Ibom suka karba, wadanbda suka rage sun kuma kai 286, 928,” inji shi.
Ya kuma ce, za a ci gaba da rarraba katin a dukkan mazabu kamar dai yadda aka saba, za kuma a dakatar da raba katin ne a ra=nar 16 ga watan Janairu zuwa ranar 21 ga watan Janairu 2019
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!