Connect with us

LABARAI

Jikan Shehu Inyass Na Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar AGA

Published

on

Dan takarar neman Gwamnan Kano karkashin jam’iyyar “All Grasroot Allience” AGA Shehu Tijjani Sani Auwalu Darma. ya nemi al’ummar jihar Kano su bashi hadin-kai da goyon baya domin kofarsa za ta zama a bude don karbar shawara da za ta kawo ci gaba ga jihar, Shehu Tijjani Sani Auwalu, wanda jika ne ga Shehu Ibrahim Inyass ya bayyana haka ne a wajen taron kaddamar da takararsa da aka gudanar a dakin taro na masallacin Shehu Ahmadu Tijjani dake kofar mata ya yi nuni da cewa sanya tsoron Allah shi ne abu mafifici da yake taimakawa mai mulki wajen yin adalci kuma wanan yana samuwa ne ta karbar shawarar al’umma.
Ya kara da cewa dan haka ma ya jawo malamai da mutane masu kima da suka yarda da wannan tafiya tasa domin a tafi tare akai ga nasara da za su rika bada shawara na abin da ya dace don kawo ci gaban al’umma in an kai ga kafa Gwamnati. Saboda a halin da ake ciki masu mulki suna
dauka mulki nasu ne don haka basa girmama ra’ayin al’umma sun danne ‘yan majalisu ta ba su kudade mulki ya zama na wasu tsiraru ke mulki na ganin dama ba sanya adalci da tsoron Allah a ciki.
Shehu Tijjani ya ce, shi wannan takara Allah yasa a gaba kuma duk irin ci gaba da ake tunani za a samu idan ba tsoron Allah a ciki ba abin da zai amfanar shi yasa ma aleta samun matsaloli daga shugabanci da ake a kasar nan, kuma shi mulki baya dawwama amma al’umma suna dawwama.
Ya ce, a wannan takara tasa suna da buri da shirin kyautata jin dadin al’umma na birni dana karkara musamman ma duba da halin da suke ganin al’ummar kauyuka a ciki in sun shiga. Za su bai wa dukkan kananan hukumomi hakkinsu ta yanda za su kula da ci gaban al’umma. Sannan zasu kuda ci gaban matasa da mata wanda a yanzu sai kaga ana basu kwaya a basu makamai ana bata tarbiyarsu.
Shehi ya ce, su a matsayinsu na yan darikar Tijjaniyya dama ambaton Allah da ilimi da kyakkyawar mu’amala ta tsoron Allah suke dora al’umma akai kuma za su ci gaba da kyauta tarbiyar matasa domin su zama nagari masu anfani ga al’ummarsu. Duk da cewa jam’iyyar ta su ta AGA tana da rinjayen goyon bayan yan’darikar Tijjaniyya,wannan ba yana nufin an kebanceta da wata darika bane ko kungiyar addini kowa yana da dama a cikinta hasalima jam’iyyar ba musulmi ne suka kafata ba, kuma shugabaninta ma ba ‘yan darikar bane akwai kuma kiristoci da kungiyoyi daban-daban a cikinta.
Shehi Tijjani Sani Auwalu ya ce, dalilinsu na dauko jam’iyyar AGA dukk da cewa ba fitacciya bace a baya saboda manyan jam’iyyu yan jari hujja sun mamayesu basa bari masu kishi da dason ci gaba su nemi takara shi yasa suka dauko wannan jam’iyya ta AGA kuma yanzu haka tana bunkasa suna da ‘yan takara a cikinta a nan Kano sama da 50 da za su shiga zabe mai zuwa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!