Connect with us

LABARAI

Kamfen Din PDP A Jos: Atiku Ya Yi Ta’aziyyar Wadanda Suka Mutu A Hadari

Published

on

Dan takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar PDP, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a jiya yai ta’aziyyar magoya bayansa biyu da suka rasu a sakamakon hatsarin mota, wadanda suka mutu sun hada da Misis Christy Yelick Dungtou da Mista Donatus Morkwap, sun rasu ne bayan gangamin yakin beman zaben da aka gudanar a garin Jos ta jihar ta jihar Filato.
Ya kuma bayana cewa, daya daga cikin wanda hatsarin ya rutsda da su, mai suna Mista Kwalmi Julius, wanda kuma ya ji mummunan ciwo a halin yanzu an ka shi babban asibitin garin Shendam don ci gaba da karbar magani.
A sanarwa da jami’in watas labaran Atiku, Paul Ibe, ya raba wa manema labarai, ya ce, “Mun samu labarin rasuwa Misis Christy Yelick Dungtou da Mista Donatus Morkwap, ‘yan kungiyar yakin neman zabenmu a hatsarin mota da ya auku a kan hanyarsu na zuwa gagganmi yaki neman zaben dan takarar shugabancin kasar nan, Atiku Abubakar ranar Asabar.
“Miss Dungtou ta rasu a nan take yayi da kuma Morkwap ya rasu a kan hanyar zuwa babban asibitin garin Barkin-Ladi don yi masa magani.
“Yayin da kuma Mista Kwalmi Julius, daya daga cikin wadanda suka ji ciwo a hatsarin kuma yana karbat magani a asibitin gwamnantin jihar Filato, haka kma wasu mutum biyu na karbar magain a wani asibitui na garin Shendam.”
Ya kuma bayyana cewa, kungiyae yakin neman zaben Atiku na tuntubar jami’an kungiyar yakin meman zaben tuni kuma aka wuce da gawarwakin wadanda suyka mutu zuwa baban asibitin karamar hukumar Shendam ta jihar Filato.
“Maigirma Atiku Abubakar yana mika ta’aziyyarsa ha iyalan wadanda suka mutu tare da faan Allah Ya gafarta musu ya kuma ba wadanda suka ji ciwo sauki da gaggawa.
Tsohon mataimakin kasar ya kuma umurci kungiyar yakin neman zabensa da su tabbatar da an dauki nauyi biyan dukkan kudaden da ake bukata na magani ga wadabda suka ji ciwo tare kuma da daukin dukkan nauyin abubuwan da ake bukata na jana’izar wadanda suka mutu.
“Dan takarar shugabancin kasar nan na jam’iyyar PDP ya kuma bayyana cewa, yana sane da sadarkarwa da magoya ba7ansa ke yi a fadin kasar nan, ya kuma yi alkawarin dawo da shugabancu na gari a kasar nan, ya kuma yi aljawarin cewa, sadarkarwar da suke yi ba zai tafi a banza ba.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!