Connect with us

SIYASA

Magoya Bayan Dogara Da Jam’iyyu Sun Yi Bore Kan Kokarin Sauya Cibiyar Tattara Sakamakon Zabe

Published

on

Magoya bayan Kakakin majalisar tarayya, Honorabul Yakubu Dogara sun gudanar da zanga-zangar lumana suna masu kin amincewa hadi da yin bore kan kokarin da hukumar zabe INEC take da shi na canza cibiyar tattara sakamakon zaben mazabar Bogoro, Dass da kuma karamar hukumar Tafawa Balewa daga garin Zwall zuwa Dass.
Zanga-zangar wacce suka yi ta a karshen makon jiya, daga cikin wadanda suka shiga cikin zanga-zangar har da jam’iyyun adawa daban-daban, masu ruwa da tsaki musamman a mazabar Dass, T/Balewa da Bogoro, inda suka nuna cewar wata shirin markashiya ce ake shirin cimmawa domin yin magudi a zaben 2019 da ke tafe.
Masu nuna kin amincewarsu kan hakan, sun mamaye ofishin hukumar zabe INEC da ke Bauchi, inda suka gabatar da takardar gargadi da neman INEC ta dakatar da wannan yunkurin nata ko kuma su dauki matakin da doka ta basu na kai kara zuwa ga shugaban hukumar zabe ta kasa, suna masu shaida cewar wannan yunkuri ne kawai na kawo wa Kakakin majalisar tarayya cikas a cikin nasarorinsa.
Da yake jawabi a ofishin INEC a madadin dukkanin jam’iyyun da suka ki amincewa da wannan yunkurin, Honourable Isa Babayo Tilde shugaban shiyyar Bauchi ta Kudu na jam’iyyar PDP, ya shaida cewar, “Muna son INEC ta kasance mai kawo ci gaba ne ba mai yunkurin sauya matsugunin muhallin tattara sakamakon zaben Dass, T/Balewa da Bogoro daga Zwall zuwa Dass ba, wanda barin cibiyar nan a inda take shi ne zai tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma hakan shine zai tabbatar da adalci wa jama’an mazabar,” Inji shi
Ya shaida cewar gwamnatin tarayya ta asassa mazabar Dass, T/Balewa da Bogoro ne tun a shekarar 1979, wance shalkwatan yankin ke karamar hukumar Tafawa Balewa, inda aka sauya wa shalkwatan mazuguni zuwa Bununu a shekarar 2013 a sakamakon wasu dalilai, amma cibiyar tattara sakamakon zabe na nan a Tafawa Balewa duk da an yi kokarin sauya masa matsuguni zuwa Dajin duba da matsalolin tsaro, “Masu ruwa da tsaki suka zauna suka tattauna komai da komai daga karshe aka bar cibiyar tattara sakamakon zaben nan a garin Zwall, har zuwa yau kuma a wajen yake, amma abun takaici sai yanzu da daf zabe wai an fara kokarin sauya wannan cibiyar zuwa Dass, mu ba za mu yarda ba sam,” Inji shi
Ya nemi cewar koda INEC tana da wasu dalilanta, akwai matakai na doka da ka’idojin sauya cibiyar tattara sakamakon zabe, don haka ne ya nemi INEC din ta sauya yunkurinta.
Wani tsohon dan majalisar tarayya, Honourable Dauda Garba Bundot ya shaida cewar an sauya cibiyar tattara sakamakon zabe ne daga Tafawa Balewa zuwa Zwall domin wanzar da zaman lafiya da tsaro a lokacin zamanin gwamna Isa Yuguda, “A lokacin da Yuguda ya yi kokarin sake dauka cibiyar, an kai ga har zuwa kotu, daga bisani aka nemi a tattara dukkanin masu ruwa da tsaki a zauna wuri guda wanda shine aka bar zancen a garin Zwall,” Inji shi.
Da yake amsar wasikar korafin a madadin kwamishinan hukumar zabe na jihar Bauchi, babban jami’in hulda da jama’a na hukumar, Mohammed Yahaya Salihu ya bayyana cewar za su daukaki korafin zuwa ga wuraren da abun ya shafa, inda ya tabbatar da cewar za su kuma yi adalci wa kowa da kowa.
Ya nemi masu boren su kwantar da hankalinsu domin a cewarsa za su tabbatar da komai ya tafi daidai.
Jam’iyyun da suka ki amincewa da wannan yunkurin sun hada da PDP, SDP, PRP, APP, PDM, CAP, NNPP da kuma GPN dukkaninsu shugabaninsu inda wasu kuma sakatarorin jam’iyyun daga mazabar Dass, T/Balewa da Bogoro suka sanya hanu kan takardar da aka gabatar wa INEC na kin amincewa da matakin sauya cibiyar kawo sakamakon zabe na mazabar.
Jam’iyyun sun shaida cewar suna fargabar sauya cibiyar tattara sakamakon a daidai wannan lokacin da ake gaf da gudanar da zaben 2019, suna masu cewa kila dai akwai wata shiryayyiyar manufa ta yin magudi ne, sun kuma kara da cewa a bar musu cibiyarsu a inda aka cimma matsaya tun a lokacin baya, kana sun kara da cewa garin Zwall tana kan babban titi ne wanda ya fi saukin hada kananan hukumomi ukun da suke mazabar.
Jam’iyyun sun ce, hakki ne akan hukumar zabe ta tabbatar da yin adalci da kuma gudanar da zabe mai sahihanci ba kawai ta maida damarta wajen kokarin janyo rikici ko tashin hankali a bisa wata boyayyiyar dalili ba, sun ce, wannan yankin na mazabarsu ta samu kwanciyar hankali da zaman lafiya don haka suna gargadi kada kuma a kawo musu wasu abubuwan da za su wargaza wannan zaman lafiyar da suke mora.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!